Jihar Kwara Na Yunkuri Hana Tserewar Likitoci Zuwa Kasashen Ketare
Published: 26th, January 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa.
Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin.
A cewarta gwamnatin ta amince da biyan Asusun Horar da Likita masu neman kwarewa da sauran abubuwan karawa likitoci gwarin gwiwa.
Dokta El-Imam ta bayyana cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen ganin dukkan ma’aikatan jinya sun yi fice a aikin da suka zaba, domin dakile yawan barin kasan nan da likitoci ke yi zuwa kasashen waje.
Kwamishinan, ya yi kira ga kungiyar da ta ziyarce ta, da ta fahimci kokarin Gwamnan ta hanyar lallashin mambobin kungiyar, su yi hakuri da gwamnati, ya kara da cewasaura kiris haka ta cimma ruwa wajen biya musu bukatunsu.
A nasa bangaren shugaban kungiyar likitocin Najeriya Farfesa Mohammad Aminu ya yabawa gwamnatin jihar bisa ginawa da kuma gyara cibiyoyin kiwon lafiya domin bunkasa samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Farfesa Aminu ya kuma yi kira ga gwamnati da ta yi aiki tukuru domin ganin an shawa kan likitoci sun daina tserewa suna barin kasan nan.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kebbi Ta Kashe Naira miliyan 67 Wajen Biya Sadakin Ma’aurata 300
Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsaya a matsayin wakilin na angwaye yayin da Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar Muhammad Iliyasu Bashar murabus ne ya tsaya a matsayin wakilin na amaren.
Gwamna Nasir Idris, yayin da yake godewa uwargidansa Hajiya Nafisa Nasir Idris bisa wannan shiri a karkashin gidauniyarta ta “Asusun NANAS ”, ya yi alkawarin bayar da goyon baya da kuma ci gaba da gudanar da shirin na shekara-shekara domin amfanin al’ummar Kebbi, ya kuma shawarci ma’auratan da su kasance masu adalci da mutunta ra’ayin juna.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku-Bagudu, ya bayyana taron a matsayin tunatarwa ga daidaikun mutane a cikin al’umma da su rika duba kansu tare da tambayar kansu nawa suka taimaka wajen yin aure a yankunansu.
Shima da yake jawabi, sakataren jam’iyyar APC na kasa, Dr Tajuddeen Bashiru, ya lura cewa, ma’auratan ba aure kadai suke yi ba, har ma gwamnatin jihar ta basu karfin gwiwa.
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Kebbi ba wai kawai ta aurar da ma’aurata 300 ba, amma tana baiwa iyalai 300 damar dogaro da kai.
Gwamnatin jihar Kebbi, ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na ware naira miliyan 54 na sadakin ma’aurata 300, kayan daki, kayan abinci da duk wani nauyin da ya rataya a wuyan aure in ban da wurin kwana.
Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, Sheik Professor Mansur Sokoto, Sheik Professor Mansur Isa da Sheik AbdurRahman Isa-Jega na daga cikin malaman addinin musulunci da suka shaida bikin.
COV/Abdullahi Tukur