An tsare mutane shida a gidan yari saboda karya dokar kare muhalli ta Taraba.
Published: 26th, January 2025 GMT
Shugaban kotun tafi da gidanka na jihar Taraba, Useni Galadima, ya tasa keyar wasu mutane shida gidan yari bisa samunsa da laifin karya dokar zartarwa mai lamba biyar, 2023, wanda gwamna Agbu Kefas ya bayar.
Wanda ake zargin, Suleiman Musa mai shekaru 30, daga Jos, jihar Filato; Adamu Umar mai shekaru 40 daga Bauchi, jihar Bauchi; Usman Umar Danburam, 35, daga Darazo, Jihar Bauchi; Ibrahim Abdullahi, mai shekaru 50, daga Mina, Jihar Neja; Aminu Mohammed, 40; da Adamu Abdul’aziz mai shekaru 46 daga jihar Taraba, an kama su ne a ranar 17 ga watan Janairun 2025.
An same su dauke da kayayyaki dama da kuma wasu duwatse ake zargin masu daraja ne a wani sansani hakar ma’adinai dake Karamar hukumar Gashaka dake jihar Taraba.
Useni Galadima ya ce ikirari na wadanda ake tuhuma da kuma abubuwan da aka gabatar sun isa a gurfanar da su gaban kuliya.
Babban lauya mai shigar da kara, Barista Neirus Johnson, ya bukaci kotun da ta kwace kayayyakin tare da zartar da hukunci kamar yadda doka ta tanada.
An dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Junairu, 2025, domin ci gaba da wannan shari’a.
KARSHE/JAMILA ABBA/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gobe take Sallah a Nijeriya — Sarkin Musulmi
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.
Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi.
Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.