Ƴan Syria da suke komawa gidajensu bayan yaƙin basasar ƙasar ya yi sauƙi a sanadiyar hamɓarar da gwamnatin Assad, suna cike da fargabar bama-bamai da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.

Aƙalla mutum 144, ciki har da ƙananan yara 27 ne suka rasu a sanadiyar ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin daga lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, kamar yadda ƙungiyar Halo Trust ta ruwaito.

Jami’an tsaron White Helmets na Syria sun bayyana wa BBC cewa yawancin waɗanda suka rasu manoma ne da suka fara komawa gonakinsu.

Hassan Talfah, wanda yake jagorantar sashen tsince bama-bamai a arewa maso yammacin ƙasar, ya ce nau’in UXO waɗanda ba a ƙarƙashin ƙasa suke ba, sun fi sauƙin sha’ani, sannan ya ce tsakanin Nuwamban bara zuwa 3 ga Janairu sun ctsince aƙalla bama-bamai 822.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

HKI Ta Yi Barazanar Shiga Rikicin Da Ya Barke  A Garin Jarmana Na Kasar Syria

Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojoji a shirye suke su shiga cikin rikicin da ya barke a garin Jarmana dake kusa da birnin Damascuss na kasar Syria domin kare ‘yan Duruz.

Ofishin Fira ministan HKI Benjemine Netanyahi ya fitar da sanarwa a jiya Asabar da marece, yana ce; Netanyahu da ministansa na yaki Yesra’il Kats sun bayar da umarni ga sojojin kasar da su kasance cikin shiri domin kare ‘yan Duruz a garin Jarmana dake bayan binin Damascuss.

Ofishin watsa labarai na ministan yakin na HKI ya ce; Nauyi ne a wuyanmu mu kare ‘yan’uwanmu Duruz a cikin Isra’ila, da kuma hana a cutar da su a cikin Syria, don haka za mu dauki duk wani mataki da ya dace domin kare tsaronsu.”

 Bayan kashe jami’an tsaron kasar Syria biyu, jami’an tsaron sun shiga cikin garin domin neman masu laifi,lamarin da ya haddasa taho-mu gama da makamai.

Kamfanin dillancin labarun Reuters, ya bayyana cewa; HKI ta bukacin Amurka da ta daina yin matsin lamba ga Rasha ta bar Syria saboda ta kalubalanci kwadayin Turkiya na shimfida nata ikon a wannan kasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Junbilat: ‘Yan Sahyoniya Suna Son Tarwatsa Kasar Syria
  • Jagora: Iran Tana Fuskantar  Makiya Na Waje Kafirar Da Munafikai
  • Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha
  • HKI Ta Yi Barazanar Shiga Rikicin Da Ya Barke  A Garin Jarmana Na Kasar Syria
  • Kare ya ta da gobara a gida
  • An kama ɓarayin waya a Kano
  • Za Mu Doke Atletico Madrid Har Gida, Hansi Flick
  • Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila
  • Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa
  • HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato