Jami’an Kiwon Lafiya Mazauna Saudiyya Sun Gudanar Da Aikin Ido Kyauta Ga Al’ummar Jihar Jigawa
Published: 26th, January 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse.
Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin.
Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane 300 da aka baiwa
gilashi.
Kazalika, mutane 400 kuma suka sami maganin ciwon ido.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ta Bada Tabbacin Tsaro A Bukin Ista
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gombe, Bello Yahaya ya bayar da umarnin tura isassun jami’ai a fadin jihar domin samar da isasshen tsaro kafin bukin Easter, da kuma bayan bikin Easter.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a Gombe.
A cewarsa, an tura jami’an dabarun dakile hare-hare zuwa muhimman wuraren da suka hada da wuraren ibada, wuraren shakatawa, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a.
Ya kuma ce, kungiyoyin sintiri da jami’an tsaron cikin za su kasance a kasa domin sanya ido kan ayyukan da kuma gaggauta daukar matakin magance duk wata matsala idan ta taso.
Kwamishinan ya lura cewa rundunar tana aiki tare da hadin gwiwar ‘yan uwa jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma domin kula da su a cikin doka da oda yayin da ake ƙarfafa ‘yan ƙasa su kasance masu bin doka da oda kuma su kai rahoton duk wani abin da ake tuhuma ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
HUDU/GOMBE