Za a raba tallafin karatu ga Dalibai 100 a Mazabar Chikun da Kajuru
Published: 26th, January 2025 GMT
Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati.
Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau.
Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren.
Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin manofofin da yake da su ba ga al’ummar sa ba, yana nuna cewa yana son ganin an sami al’umma mai ilimi.
‘Yan kwamitin sun hada da Hon. Dauda Abdulkadir Kujama a matsayin shugaba Sai wakilan kwamitin da suka hada da Hon Ibrahim Garba Danmajen Chikun da Hon. Ibrahim Umar.
Sauran su ne Mrs. Rebecca Akapson da Hon. Daniel Sisin Kobo
Saifu Adamu Bawa Kajuru sai Hon. Ganaka James Kogi da aka ba sakataren kwamitin.
Wanda ke bukatar samun wannan tallafi sai ya sauke wannan takarda ya cika ya kawo.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ramadan: Hon Jaji Ya Ƙaddamar Da Tallafin Abinci Ga Mutane Sama Da 500,000 A Zamfara
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp