Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar.

Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa.

Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Jigawa a shekarar da ta gabata ta lalata gine-ginen makarantu 115, wanda hakan ya kawo cikas ga  dalibai.

Ya bayyana alhininsa kan yadda lamarin ya haifar da tsawaita rufe makarantu,  wanda ya shafi karatun  yara sama da 92,518 a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.

“A jihar Jigawa, ambaliyar ruwan da ta afku a shekarar da ta gabata ta lalata  gine-gine da kayayyakin makarantu 115, wanda hakan ya sa ba za a iya amfani da su ba.

“Hakan ya haifar da tsawaita rufe makarantu da kuma rashin wadatar ilimi ga dalibai kimanin 92,518, wadanda 43,813 daga cikinsu mata ne, yayin  da 48,705 kuma yara maza ne, a fadin kananan hukumomi 27 na jihar,” Mista Farah.

Ya yi nuni da cewa, UNICEF tare da tallafi daga ofishin kula da harkokin kasashen waje da na kungiyar kasashen renon Ingila da ke  Burtaniya, na tallafa wa gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa, don samar da yanayin koyo mai kyau domin rage tasirin sauyin yanayi da ya shafi koyon ilimia makarantu.

Ya bayyana cewa, a shekarar 2024, UNICEF ta dauki nauyin matasa dubu daya, wadanda 350 daga cikinsu sun fito ne daga jihar  Jigawa, yayin da 650 kuma suka fito daga Katsina, don dasa bishiyu 300 a yankin hamada da kuma wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa a jihohin biyu, domin dakile tasirin sauyin yanayi.

“Tare da goyon bayan abokan hulda da suka hada da ofishin kula da harkokin kasashen waje, da na kungiyar kasashen renon Ingila da ke Birtaniya, UNICEF na tallafawa jihohin Kano da Jigawa don samar da yanayin koyo mai kyau, don rage tasirin da  sauyin yanayi ke haifarwa”. 

Shugaban na UNICEF ya kuma bayyana cewa a shekarar da ta gabata asusun ya gina cibiyoyin kula da tsaftar ruwa da tsaftar muhalli (WASH) a makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a wuraren da ake bukata a cikin jihohin uku.

Ya ce asusun ya kuma gina tare da gyara wuraren tsaftar muhalli a makarantu 33, inda aka gina 25 a jihar Kano, sauran 8 kuma a jihar Jigawa, wadanda yara 39,432 ke amfani da su a jihohin biyu.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da ƙananan sana’o’i, waɗanda al’umma ke dogaro da su don biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Irin waɗannan sana’oi sun haɗa da saƙa, jima, fawa, suyan ƙosai ko masa da dai sauransu.

A da can masu waɗannan sana’o’i sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da hajojinsu ko kuma waɗanda suka samu a yayin da suka ɗauki tallar kayan sana’ar tasu.

Sai dai a wannan zamani masu waɗannan sana’o’i na fuskantar barazana daga wurin ’yan zamani ’yan bana bakwai da suka shigar da zamani ciki suke neman kwace musu ragama ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta wajen tallata hajojinsu.

NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan hanyoyin da mutane za su haɓaka sana’oinsu ta hanyar amfani da kafofin sada zumuntar.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Baffa Bichi, Kabiru Rurum, Sha’aban Sharada Da Wasu Sun Koma Jam’iyyar APC
  • Kare-Karen Haraji Ba Zai Bunkasa Arzikin Amurka Ba
  • Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
  • Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
  • An kama wasu mata na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace
  • An Umurci Sojoji Su Kawarda ‘Yan Bindiga Daga Kwara Da Niger A Cikin Wata Daya
  • NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci
  • Ƙasurgumin Ɗan Fashin Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Mutu Bayan Arangama Da ‘Yansanda A Kano
  • DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa
  • Kungiyar Hamas Ta Bukaci Goyon Baya Daga Sauran Falasdinawa Na Gabar Yammacin Kogin Jordan