UNICEF Zai Shawo Matsalar Yawan Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta A Arewa Maso Yammacin Najeriya
Published: 26th, January 2025 GMT
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar.
Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025.
Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da kuma miliyan daya da dubu dari daya da saba’in da shidd, da dari tara da goma sha takwas(1,176,918), a matakin kananan makarantun sakandare, wanda ya bayyana a matsayin abin ban tsoro.
Ya gano wasu kalubalen da ke ci gaba da faruwa a halin da ake ciki baya ga makaranta, da suka hada da rashin isassun kudade, da rashin kula da al’adu, da rashin isassun kayayyakin more rayuwa a makarantu, da karancin ma’aikata da gudun hijira sakamakon ambaliyar ruwa da sauran illolin sauyin yanayi.
“Yayin da Arewa maso Yammacin Najeriya ta kasance ta biyu a kasar da ba a zuwa makaranta, lamarin da ake fama da shi a jihohin Kano da Jigawa da Katsina yana da ban tsoro.
“Abin da ya kara ta’azzara shi ne sakamakon rashin ingantaccen ilimi ga yaran da suka yi sa’ar shiga makaranta.
“A halin yanzu akwai kimanin yara miliyan goma da dari biyu a matakin firamare da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, inda kashi 16 cikin 100 sun fito ne daga jihohin Kano, da Jigawa da Katsina, a cewar rahoton MICS na shekarar 2021.
“Kusan yara miliyan daya ne ba sa zuwa makaranta a jihar Kano da jimillar mutane 989,234, yayin da a Jigawa ana da jimillar 337,861 sai jihar Katsina da ke da yara 536,112 da ba sa zuwa makaranta.”
Mr Farah ya bukaci gwamnatocin jihohin Kano, da Jigawa da Katsina da su daidaita kasafin kudi tare da fitar da su a zahiri ga bangaren ilimi daidai da abin da ake bukata na Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa na SDG da ma’aunin Hukumar kula da Ilimi, da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) don ingantacciyar sakamako a fannin.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin wadannan jahohin da su tunkari kalubalen samun ilimi ta hanyar fadada abubuwan more rayuwa a makarantu da daukar kwararrun malamai da shigar da makarantun kur’ani a cikin tsari na yau da kullun.
Daga Isma’il Adamu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu
Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp