Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin.

Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar.

Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban.

Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban.

Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar.

Wakilinmu ya aiko mana da rahoton cewar, an gudanar da rabon tallafin wanda ya hada da tallafin karatu ga matasa 80 da aka sama musu guraben karatu a manyan jami’o’i da kwalejoji a faɗin kasar nan, da rabon babura ga mutane 30, sai keken ɗinki da aka rabawa mata 30.

Kazalika, an raba kekunan hawa 30 ga ɗalibai, da injin niƙa guda 10 da aka rabawa matsakaitan ‘yan kasuwa.

Sai kuma tallafin jari na naira dubu dari 2 da aka rabawa ‘yan kasuwa har su  20 da tallafin jari na naira dubu 100 ga ƙananan ‘yan kasuwa guda 20.

Sauran su ne tallafin jari na naira dubu hamsin hamsin ga mutane 30, da kuma bayar da naira dubu ashirin ashirin ga mutane 100, domin rage radadin halin da ake ciki, da rabon shagunanan tafi da gidanka guda 3 ga matasa masu kasuwanci.

Har ila yau, an raba babura masu kafa 3, na daukan kaya guda 2 ga matasa, sai kuma bayar da mukullin gidaje masu ɗaki biyu ga matasa guda 4 daga sassa daban-daban na karamar hukumar Sule Tankarkar.

A don haka, Gwamnan ya yi kira ga sauran shugabannin ƙananan hukumomi na jihar da su yi koyi da irin wannan gagarumin aikin  na Tasiu Adamu domin al’umma su ci gaba da sharbar romon mulkin dimokradiyya.

Ya bayyana cewar irin waɗannan ayyuka ne ke taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci da samar da ayyukan yi ga jama’a.

Taron ya samu halartar jama’a daga sassa daban-daban na jihar, inda aka bayyana wannan shiri a matsayin abin alfahari ga al’ummar Sule Tankarkar da Jihar Jigawa baki daya.

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu

Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia.

Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu.

“Kamar yadda aka bayyana a ranar Laraba 26 ga watan Maris 2025, jimillar kuɗin da aka tattara sun kai Naira miliyan 839. Bisa ga kididdiga da aka yi, kowanne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kai tsaye zai karɓi kimanin Naira miliyan huɗu.

“Ga waɗanda suka rasu, za a ba da kuɗin ga iyayensu ko magadansu, yayin da waɗanda suka tsira za su karɓi nasu da kansu.

“Kayan tallafin da aka riga aka tara, musamman abinci da sauran kayayyakin bukata, tuni an raba su ga waɗanda suka shafi lamarin“, in ji shi.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa akalla mutane 210 ne lamarin ya ritsa da su, inda 100 daga cikinsu suka mutu nan take.

“An tabbatar da cewa mutane 33 daga cikin waɗanda suka rasu magidanta ne, kuma 31 daga cikinsu sun bar ‘yaya. Jimillar matan da suka rasa mazajensu sakamakon lamarin sun kai 42, yayin da yaran da suka zama marayu suka kai 133″, in ji Gwamna Namadi.

A yayin jajantawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamnan ya yi kira ga direbobin manyan motocin dakon mai da sauran masu amfani da tituna su kasance masu taka tsantsan domin gujewa sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.

“Iftila’in da ya afku a Majia ya koyar da mu darussa masu yawa, wanda muke fatan jama’a da masu ruwa da tsaki, musamman ma waɗanda ke harkar sufuri, za su dauki darasi“. Inji shi.

Gwamnan ya kuma shawarci waɗanda suka karɓi tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, musamman wajen kafa sana’o’i.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah
  • Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah
  • Karamar Hukumar Jahun Ta Karrama Hakimai Da Limamai Da Kayan Sallah
  • Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah
  • Karamar Hukumar Jahun Ta Bada Tallafin Noman Rani Ga Manoma 300
  • Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu
  • Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
  • Kungiyar “White Helmets Ta” A Kasar Siriya Ta Rasha Tallafin Da Take Samu Daga USAID
  • Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah
  • Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno