Zantawa Da Shugaban Kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake
Published: 26th, January 2025 GMT
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki.
Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya.
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Saudiyya Sun Tattauna Kan Taron OIC Mai Zuwa
Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin dama batun taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC da za’ayi a cikin kwanaki masu zuwa a Jeddah.
Tattaunawar ta wakana ne ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da Abass Araghchi, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran (RII).
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan halin da ake ciki a yankin, tare da tattauna taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar OIC da za a yi a Jeddah.
Dama a kwanan baya bangarorin sun tattauna kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na kwace zirin Gaza dama tilasta wa falasdinawan yankin kaura zuwa Masar da Jordan, shirin da dukkan kasashen biyu sukayi fatali da shi.
Araghchi ya la’anci shirin na Amurka da ‘yan sahyoniya na tilastawa al’ummar Gaza komawa wasu kasashe a matsayin ci gaba da shirin ‘yan mulkin mallaka na shafe Falasdinu, yana mai jaddada bukatar daukar kwararan matakai na kasashen duniya don tunkarar wannan makirci.
Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da sauran al’ummar duniya baki daya da su dauki matakin gaggawa kan lamarin.