Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna (PPRO), DSP Mansir Hassan ba da aka tuntube shi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon shugaban hukumar NYSC ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga

Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 22 a hannun ’yan bindiga.

An sace shi ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke garin Tsiga a Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari.

Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250 Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta

Maharan sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 250 kafin su sako shi.

Sai dai bayan tattaunawa, an biya kuɗin fansa, wanda ya kai ga sakinsa.

A halin yanzu, likitoci na kula da shi a wani asibiti da ba a bayyana ba sunansa ba.

A lokacin kai harin, sama da ’yan bindiga 100 ne suka afka gidansa, suka yi awon gaba da shi da wasu mazauna yankin.

Wasu mutum biyu sun samu raunuka yayin harin, yayin da wani daga cikin ’yan bindigar ya harbi ɗan uwansa bisa kuskure, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Har yanzu, rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa kan sakin tsohon shugaban NYSC ɗin ba.

Satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaro a Jihar Katsina da sauran sassan Najeriya.

Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro na fuskantar matsin lamba wajen shawo kan wannan matsala.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ramadan: Hon Jaji Ya Ƙaddamar Da Tallafin Abinci Ga Mutane Sama Da 500,000 A Zamfara
  • Yadda ’yan bindiga suka sace ɗalibai 4 a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma
  • ’Yan bindiga sun hallaka mutum 6 a ƙauyukan Kebbi
  • ’Yan bindiga sun hallaka mutum 6 ƙauyukan Kebbi
  • Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC
  • Za Mu Doke Atletico Madrid Har Gida, Hansi Flick
  • Iran Da Haddiyar Daular Larabawa Sun Gudanar Da Taron Kwamitin Siyasa Da Al-adu Na Kasashen Biyu
  • ‘Yansanda Na Farautar Wadanda Suka Kashe Dalibi A Katsina
  • Tsohon shugaban hukumar NYSC ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Nemi Goyon Bayan Sarkin Zazzau Don Nasarar Aikin Hajjin Bana