Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo.

Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere.

Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka.

An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni a shekarar 2024, matakin da ya bayyana cewa, al’adun bikin na kara yaduwa zuwa duk fadin duniya zuwa wani sabon matsayi.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Taimakon Soji Da Amurka Ke Bai Wa Taiwan

A yau Laraba, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina bai wa Taiwan makamai, ta kuma guji yin kafar ungulu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin Taiwan.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa kullum, lokacin da aka tambaye shi game da rahotannin da ke cewa, gwamnatin Trump ta bayar da dalar Amurka biliyan 5.3 na taimakon da kasar ke bai wa kasashen waje da aka dakile a kwanan baya, wanda ya hada da dalar Amurka miliyan 870 da aka kebe a kan sha’anin tsaro na Taiwan.

A cewar Lin, Sin ta damu matuka game da ire-iren wadannan rahotanni, yana mai nuni da cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana jaddada adawa da taimakon soja da Amurka ke bai wa yankin Taiwan na kasar Sin, saboda irin wannan hali ya saba wa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da kuma sanarwar hadin gwiwa guda uku wadanda Amurka da Sin suka fitar, tare da keta ‘yancin kan kasar Sin da muradunta na tsaron kasa, kuma hakan na aikewa da mummunan sako ga dakarun ‘yan aware masu neman wai ‘yancin kan Taiwan. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Zama Zakara A Damben Gargajiya Ta 2025 UWW Wanda Aka Gudanar A Kasar Albaniya
  • Habasha Da Somaliya Sun Tattaunawa Hanyoyin Sake Mayar Da Alaka
  • Kasar Philippines Za Ta Dandana Kudarta Game Da Gudummawar Soja Da Amurka Ta Ba Ta
  • Kasashen Habasha da Nijar sun tattauna kan inganta hadin gwiwar soji da tsaro
  • Aljeriya Ta Yi Watsi Da Barazanar Faransa
  • Habasha Da Somaliya Sun Cimma Yarjeniyoyin Fahimtar Juna A Tsakaninsu
  • Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe
  • Jum’ar Nan Ce Duban Farin Na Watan Ramadan – Mai Alfarma Sarkin Musulmi
  • Majalisar Dattijan Aljeriya Ta Soke Duk Wata Hulda Da Majalisar Dattijan Faransa
  • Sin Ta Yi Allah Wadai Da Taimakon Soji Da Amurka Ke Bai Wa Taiwan