An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano
Published: 26th, January 2025 GMT
An gudanar da taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi kan barazanar harin ’yan ta’adda a Jihar Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ɗariƙar Tijjaniyya daga sassan Nijeriya daban-daban sun halarci taron Maulidin na Shehu Ibrahim Inyas na shekara-shekara da aka gudanar a Filin Wasa na Sani Abacha da ke ƙwaryar Birnin Dabo.
Sai dai tun a jiya Juma’a ce mai magana da yawun ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar da sanarwa mai ɗauke da gargaɗin cewa ’yan ta’adda na shirin kai hari a jihar saboda haka jama’a su ƙauracewa duk wani taro da shiga cunkoso.
Daga bisani Kwamishinan Labarai na Jihar Kano, Abdullahi Waiya, ya fitar da sanarwar cewa babu makawa sai taron ya gudana.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba ta da labarin wata barazanar tsaro, don haka babu dalilin dakatar da taron ko tunanin mugun abu zai faru a wurin taron wanda aka shafe shekaru 39 ana gudanarwa duk shekara da mahalarta daga duk faɗin Nijeriya kuma an cika ka’idoji wajen shirya shi bana.
Bayan wannan martani da Kwamishinan ya yi ne rundunar ’yan sandan ta lashe amanta da cewa za ta bayar da cikakken tsaro a wurin taron.
Taron Maulidin karo na 39 ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima wanda ya jinjina wa ’yan ɗariƙar Tijjaniyya da suka kasance jakadun haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi.
Shettima wanda ya kasance babban baƙo a yayin taron, ya bayyana ɗarikar Tijjaniyya a matsayin wadda ta yi tsayin-daka wajen koyar da addinin Islama a bisa tafarki madaidaici tsawon shekaru da dama.
Shettima wanda Babagana Fannami ya wakilta, ya jaddada irin jajircewar da ɗariƙar Tijjaniyya ta yi wajen koyar da kyawawan ɗabi’u na fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
A nasa ɓangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya kasance mai masaukin baƙi a yayin taron, ya yaba wa ɗariƙar Tijjaniyya musamman dangane da tabbatar da haɗin kai tsakanin sauran ɗariƙu a ƙasar.
Sarki Muhammadu Sanusi II wanda kuma shi ne shugaban ɗariƙar Tijjaniyya a Nijeriya, ya yi addu’ar haɗin kan musulmi a duniya tare da sauran mabiya addinai da aƙidu daban-daban.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ta Jihar Edo na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya.
A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya.
Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus.
Gwamnan Edo ya kai ziyarar jaje KanoGwamnan Kano ya karɓi baƙuncin takwaransa na Edo, Monday Okpebholo wanda ya ziyarci jihar domin jajanta wa gwamnati da al’ummar dangane da kashe mafarautan da wasu ’yan sa-kai suka jagoranta a jiharsa.
Da yake sake bayyana takaicinsa, Abba ya buƙaci gwamnan na Edo ya gaggauta gurfanar da waɗanda aka kama kan kisan matafiyan a bainar jama’a.
Abba ya kuma yaba wa yadda Mista Okpebholo ya gaggauta tashi-tsaye kan lamarin da a yanzu har an cafke wasu mutum 14 da ake zargi da aika-aikar.
‘Muna so a nuna wa duniya fuskokin mutanen da aka kama’Sai dai gwamnan na Kano ya ce “bayan kama su muna kuma so a yi holensu a bainar jama’a domin duniya ta ga fuskokin waɗanda suka yi wa ɗanyen aiki.” Ya nanata cewa Jihar Kano tamkar wata cibiya ce ta zaman lafiya “saboda haka muna gargaɗin duk ’yan Nijeriya cewa ƙasar nan ta kowa ce.”
Ya buƙaci shugabanni da su haɗa kai wajen ganin ba a sake maimaita irin wannan mummunan lamari ba a ko’ina a faɗin ƙasar, “saboda haka muna kira mahukunta sun ɗauki mataki mai tsauri a kan irin wannan.”
Da yake nasa jawabin, Gwamna Okpebholo ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an bi kadin rayukan da aka kashe, yana mai cewa a halin yanzu tuni an kama wasu mutum 14 da ake zargi kuma za a miƙa su Abuja domin ci gaba da bincike.
Kazalika, ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin Hausawa da duk wasu ƙabilu da ke zaune a jihar ta Edo.
Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa — Gwamnatin KanoGwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar Edo.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin saƙonsa na barka da sallah kamar yadda mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a jiya Lahadi.
Tun a jiya ne daman wasu majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano ta ce ana kuma sa ran karɓar baƙuncin Gwamnan Edo domin jajanta wa gwamnatin da kuma iyalan waɗanda lamarin ya shafa.
Al’ummar Edo a Kano sun yi Allah wadai da lamarinƘungiyar al’ummar Edo mazauna Jihar Kano ta yi tir da faruwar lamarin, tana mai neman da a bi wa waɗanda lamarin ya shafa haƙƙinsu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Mista Philip Tomon ya fitar, ya jajanta wa iyalan mafarautan da aka yi wa kisan gillar yana mai kiran mahukunta da su tabbatar an yi adalci a lamarin.
Ƙungiyar Mafarauta ta jingine zanga-zangaA wata sanarwa da Sakataren Ƙungiyar Mafarautan Kano, Usman Mu’azu Abdullahi Yakasai ya fitar, ya ce sun jingine zanga-zangar da suka shirya gudanarwa.
Sai dai sakataren wanda aka fi sani da Alaska duk da tana cikin alhini ta jingine zanga-zangar ce bayan tuntuɓe-tuntuɓen da ta yi, inda ta miƙa wa Gwamnatin Kano ƙorafi a hukumance na neman yi wa waɗanda aka kashe adalci.
Alaska ya ce ƙungiyar ta gamsu da irin matakan da ake ɗauka wajen tunkarar lamarin, kuma tana fatan doka za ta yi aiki yadda ya kamata.
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro a jihar Friday Ibadin, biyo bayan kisan da aka yi wa mafarauta 16 ƴan asalin yankin arewacin kasar a alhamis da ta gabata.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Umar Musa Ikhilor ya fitar mai cewa an ɗauki matakin ne la’akari da bayanan da ke ƙunshe a rahoton binciken farko da aka gudanar dangane da wannan lamari, wanda ya yi matuƙar girgiza jama’a a Najeriya.
“Lura da abubuwan da suka faru a ranar ta 27 ga watan Maris na 2025 a garin Uromi na ƙaramar hukumar Esan, inda aka samu asarar rayukan wasu matafiya, Mai Girma gwamna Monday Okpebholo, ya bayar da umurnin dakatar CP mai ritaye Friday Ibadin, Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro ta jihar daga matsayinsa,’’ a cewar sanawar.
An rusa duk ƙungiyoyin ’yan bangar da ba su da rajistaHar ila yau, sanarwar da Sakataren Gwamnatin jihar ta Edo ya fitar ta ƙara da cewa an rusa ilahirin ƙungiyoyin ’yan banga da ba su da rajista a jihar, biyo bayan wannan kisa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ’yan bangar da suka aikata wannan ta’asa, suna aiki ne ƙarƙashin inuwar wata ƙungiya da ba ta da rajista, saboda haka ya zaman wajibi a ɗauki wannan mataki don tabbatar da samar da yanayi na tsaro a jihar.
Mahukuntan Edo na tattaunawa da takwarorinsu na Kano kan lamarinYanzu haka ana ci gaba da bincike dangane da wannan lamari, kuma tuni aka kama mutane 14 da ake zargi, yayin da ake farautar wasu mutane da dama da suka arce kamar dai yadda Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya ya bayar da umarni.
Gwamnatin Edo ta ce tana ci gaba da tattaunawa da dangin marigayan, da kuma mahukuntan jihar Kano, lura da cewa mafi yawan ’yan asalin jihar ne, tare da ɗaukar alƙawarin cewa za a tabbatar da adalci ta hanyar hukunta waɗanda aka sama da laifi.
Bayanan da suka fito fili bayan faruwar wannan lamari, sun tabbatar da cewa mafarautan sun fito ne daga Fatakwal da ke Jihar Ribas a hanyarsu ta zuwa Kano domin yin bukukuwan sallah a cikin iyalansu.
‘Za mu tura ababen zargin 14 zuwa Abuja’Gwamna Okpebholo a wata ziyara wannan Litinin ɗin da ya kai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau a gidansa da ke unguwar Maitaima a Abuja, ya ce ababen zargin 14 da aka kan alaƙa da kisan matafiyan za a garzaya da su Abuja domin ci gaba da bincike.
Da yake nasa jawabin, Sanatan Barau mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawan, ya yaba wa ƙwazon gwamnan kan matakan da yake ci gaba da ɗauka tun bayan faruwar wannan mummunan lamari domin ganin waɗanda ke da hannu a cikinsa sun fuskanci hukuncin shari’a.
Ya zama dole a hukunta masu laifi a lamarin — CANƘungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta yi tir da Allah wadai dangane da kisan da aka yi wa mafarauta 16 a lokacin da suke ratsa jihar Edo a hanyarsu ta komawa a arewacin ƙasar.
A sanarwar da ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Archbishop Daniel Okoh a ranar Lahadi, da farko CAN ta isar da saƙon nuna alhini zuwa ga ƴan uwa da aminan waɗanda suka rasa rayukansu, daga nan kuma ta yi kira ga mahukunta da su ɗauki matakan da suka wajaba domin tabbatar da cewa ana aiki da doka da kuma cusa wa jama’a ra’ayin yarda da tsarin shari’a na ƙasar.
Daga nan sai sanarwar ta ce ‘’alhaki ya rataya a wuyan gwamnati domin tabbatar da cewa an gudanar da bincike da nufin hukunta waɗanda ke da hannu a wannan lamari da za a iya bayyana shi a matsayin mummunan cin zarafin bil Adama’’.
Har ila Ƙungiyar ta Kiristocin Najeriya ta isar da saƙon taya murna ga al’ummar Musulmi dangane da bukukuwan sallar da suke yi bayan sun kammala azumin watan Ramadan.
Ƙungiyar Amnesty International mai fafatikar kare haƙƙin ɗan Adam ta ce dole binciken da za a yi, ya zama sanadiyar hukunta waɗanda suke da hannu a kisa tare da ƙona matafiya ’yan arewa da aka yi a garin Uromi da ke Jihar Edo.
Shugaban ƙungiyar a Nijeriya, Isa Sanusi ne ya bayyana haka, inda, “dole hukumomin Najeriya su tabbatar an gudanar da bincike a bayyane, sannan kuma binciken ya zama silar adalci ga waɗanda aka kashe da iyalansu.
“Ya kamata a riƙa bayyana yadda binciken ke gudana tun daga farko har zuwa lokacin yanke hukunci.”
Amnesty ta ce abin da ya faru Uromi na nuna yadda ake ƙara samun ƙungiyar ’yan sa-kai na garuruwan da suke kusa da manyan hanyoyi suke tare hanyoyin suna aikata ba daidai ba.
“Yadda aka daɗe ana irin waɗannan kashe-kashen na nuna akwai gazawar gwamnati wajen kare rayukan al’ummarta.”
Isa Sanusi ya ƙara da cewa Amnesty ta yi Allah wadai da kisan, sannan ya sake nanata kiransu ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin da ya dace.
Dole a kawo ƙarshen kisan gillar da ake yi wa ’yan ArewaƘungiyar dattawan arewa ta magantu kan kisan matafiya ƴan yankin arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo, inda ta ce yankin arewa ya daɗe yana haƙuri da cin kashin da ake yi masa, amma kuma an kusa ƙure su.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar.
Sanarwar ta ce, “dattawan arewa sun damu matuƙa da kisan dabbanci da rashin tausayi da aka yi wasu mafarauta ƴan arewa da suke hanyarsu ta komawa gida arewa domin bikin sallah. Muna Allah wadai da wannan aika-aikar.
“Mun daɗe muna haƙuri da irin wannan cin kashin da ake mana a kudancin Nijeriya. Dole a kawo ƙarshensa haka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dole a kama waɗanda suka aikata laifin, sannan a musu hukunci a bayyane.
“Sannan dole a biya diyyar waɗanda aka kashe kamar yadda yake a addinance, sannan dole gwamnatin Edo ta fito ta bayar da haƙuri.”
Dattawan sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Edo ta cika waɗannan buƙatun nan da kwana da 14, “idan kuma ba a ga wani mataki ba zuwa lokacin, dattawan arewa za su yi amfani da duk matakan da suka dace wajen bin haƙƙin ƴaƴanta da aka kashe.”
A bi mana haƙƙi — ’Yan uwaWakilan Aminiya sun ziyarci ƙauyen Torankawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, inda suka zanta da wasu daga cikin iyalan mafarautan da aka kashe.
Wasu daga cikin iyalan mafarautan kuma mazauna ne a ƙauyukan ƙananan hukumomin Garko, Kibiya da Rano da ke Jihar Kanon.
Tun dai bayan samun labarin faruwar lamarin ne mazauna ƙauyen Torankawa da aka sansu da sana’ar farauta suka shiga cikin alhinin da suka ce ba su taɓa faɗawa makamancinsa ba.
Shida daga cikin mafarautan da aka kashe da wani ɗaya da ya tsallake rijiya da baya sun fito ne daga ƙauyen.
Daga cikin mamatan akwai Abdulkadir Umar, wanda ya rasu ya bar mata biyu da mahaifiyarsa.
Sai kuma Zahraddeen Tanko wanda ya bar mata ɗaya da ’ya’ya huɗu da kuma Haruna Hamidan wanda shi ma ya rasu ya bar mata ɗaya da ’ya’ya huɗu.
Akwai kuma Usaini Musa wanda ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya biyu da Abdullahi Harisu wanda ya yi aure watanni huɗu da suka gabata da kuma Ya’u Umaru da Abubakar Ado da ba su kai ga yin auren ba ma.
Duk ’yan uwan mamatan da Aminiya ta zanta da su sun bayyana alhini — wasunsu cikin hawaye suna roƙon mahukunta da su bi musu haƙƙinsu.