SERAP ta maka Tinubu da NCC a kotu kan kara kudin kiran waya da data
Published: 26th, January 2025 GMT
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50.
NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.
Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya.
SERAP, ta ce wannan karin an yi sa ba bisa ka’ida ba, kuma ya saba wa doka tare da keta hakkin ’yan Najeriya na ’yancin yin magana da samun bayanai.
A cikin karar da ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, SERAP ta nemi kotu ta dakatar da aiwatar da karin kudin, inda ta ce bai halatta ba.
Kungiyar ta yi zargin cewa NCC ba ta bi ka’ida ba kuma ba ta yi la’akari da tasirin da karin zai yi a rayuwar ’yan Najeriya, wadanda da dama ke fama da tsadar rayuwa.
SERAP, ta jaddada muhimmancin samun sadarwa cikin yanayin mai sauki, inda ta ce hakan wajibi ne don bai wa mutane damar amfani da hakkinsu na ’yancin magana da samun bayanai.
Ta ce karin zai kara tsunduma mutane cikin talauci da kuma kawo nakaso ga harkar sadarwa a fadin Najeriya.
Kungiyar na rokon kotu ta bayar da umarnin dakatar da NCC, wakilanta ko kamfanonin sadarwa daga aiwatar da karin kudin.
Lauyan SERAP, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN), ya ce wajibi ne a tabbatar da adalci, bin doka da kuma yin la’akari da yanayin da mutane ke ciki, kafin yanke duk wani hukunci da zai shafi rayuwar jama’a.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu?
Rahotanni na cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya zabga wa Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, mari saboda kalaman suka da ya yi kan gwamnatin jihar.
Wasu rahotanni na cewa Ministan ya yi wasu kalamai na caccaka ga Gwamna Bala Mohammed, lamarin da ya fusata mataimakinsa ya ɗauke Ministan da mari.
An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar banaBayanai sun ce lamarin ya faru ne a cikin motar da ke dakon wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, yayin da suke kan hanyar zuwa naɗin sarauta da kuma ɗaurin auren ’yar tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abdullahi Abubakar SAN.
Aminiya ta ruwaito cewa, a Juma’ar da ta gabata ce manyan jami’an gwamnati suka halarci ɗaurin auren Khadija Muhammad, da kuma naɗin sarautar Makama Babba I da aka gudanar a Fadar Sarkin Bauchi.
Sai dai cikin wata sanarwar mayar da martani kakkausa kan lamarin, kakakin mataimakin gwamnan, Muslim Lawal, ya musanta labarin, yana mai nanata cewa ubangidansa mutum ne mai mutunci da kamala da ba zai taɓa tsoma kansa cikin irin wannan hauragiya ba.
Amma wani da abin ya faru kan idonsa kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa, Mataimakin Gwamnan ya fusata ne bayan Ministan Harkokin Wajen ya riƙa jifar Gwamna Bala Mohammed da kalamai marasa daɗi. Majiyar ta ce wannan ce ta sanya rikicin ya hautsine a cikin motar da ke dakon manyan jami’an gwamnatin zuwa Fadar Masarautar Bauchi. Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Minista Yusuf Tuggar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Sai dai ɗan gwamnan jihar, Shamsuddeen Bala Mohammed na daga cikin waɗanda suka yi farin ciki da faruwar lamarin wanda ya riƙa tashe a dandalin sada zumunta na X.
Cikin wata wallafa mai tashe da ɗan gwamnan ya ƙara yaɗawa, mai ɗauke da saƙon cewa, “Mataimakin Gwamna na farko da ya mari Minista a Bauchi. Mista Taka ka sha mari….” da sauran saƙonni makamancin wannan da suke tashe.
Ana iya tuna cewa, wannan tsamin dangantaka ya samo asali ne tun bayan da Gwamna Bala Mohammed ya riƙa sukar Shugaba Bola Tinubu kan rashin shugabanci nagari.
A cewar gwamnan, manufofin da gwamnatin Tinubu ta ƙaƙaba sun jefa al’ummar ƙasar nan cikin ƙangin talauci da tsadar rayuwa.
Sai dai a martanin da Ministan ya mayar, ya ce gwamnan na fakewa da manufofin Tinubu domin ɓoye gazawarsa da zummar samun karɓuwa wajen neman kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake zargin cewa shi kansa Ministan na fafutikar zama Gwamnan Bauchi a 2027.