HausaTv:
2025-03-31@22:23:24 GMT

Iran Da Afganistan Sun Tattauna Al-Amura Masu Muhiammaci A Kabul

Published: 26th, January 2025 GMT

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  wanda ya jagoranci tawagar yan siyasa da kuma tattalin arzikin kasarsa zuwa birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan, a yau Lahadi sun tattauna al-amura masu muhimmanci  tsakaninsu da kuma yanking aba daya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa ministan ta hadu da tokwaransa na rikon kwarya Amir Khan Muttaki a birnin Kabul inda suka tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu.

Wadanda suka hada da al-amuran kan iyakokin kasashen biyu, tsaro, ruwa da hakkin ko wace kasa kan ruwan da ke kwarara daga kasar Afganistan zuwa kasar Iran. Da batun miliyoyin yan kasar Afgansitan wadanda suke rayuwa a kasar Iran na shekaru kimani 50.

Ministocin biyu sun tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu, wadanda suka hada da makobtaka, musulunci, al-adu da sauransu. Kasashen biyu malobta ne na shekaru aru-aru.

A nashi bangaren Muttaki ya godewa kasar Iran kan daukar bakwantan miliyoyin yan kasar Afganistan, ya kuma bayyana cewa gwamnatin Taliban tana iya kokarinta don ganin sun dawo gida musamman ganin cewa al-amura sun fara kyautata a kasar.

Sannan daga karshe ya ce kasashen biyu zasu yi aiki tare don yaki da yan ta’adda a kasashen biyu musamman a kan iyakokin kasashen biyu

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu

Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia.

Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu.

“Kamar yadda aka bayyana a ranar Laraba 26 ga watan Maris 2025, jimillar kuɗin da aka tattara sun kai Naira miliyan 839. Bisa ga kididdiga da aka yi, kowanne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kai tsaye zai karɓi kimanin Naira miliyan huɗu.

“Ga waɗanda suka rasu, za a ba da kuɗin ga iyayensu ko magadansu, yayin da waɗanda suka tsira za su karɓi nasu da kansu.

“Kayan tallafin da aka riga aka tara, musamman abinci da sauran kayayyakin bukata, tuni an raba su ga waɗanda suka shafi lamarin“, in ji shi.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa akalla mutane 210 ne lamarin ya ritsa da su, inda 100 daga cikinsu suka mutu nan take.

“An tabbatar da cewa mutane 33 daga cikin waɗanda suka rasu magidanta ne, kuma 31 daga cikinsu sun bar ‘yaya. Jimillar matan da suka rasa mazajensu sakamakon lamarin sun kai 42, yayin da yaran da suka zama marayu suka kai 133″, in ji Gwamna Namadi.

A yayin jajantawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamnan ya yi kira ga direbobin manyan motocin dakon mai da sauran masu amfani da tituna su kasance masu taka tsantsan domin gujewa sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.

“Iftila’in da ya afku a Majia ya koyar da mu darussa masu yawa, wanda muke fatan jama’a da masu ruwa da tsaki, musamman ma waɗanda ke harkar sufuri, za su dauki darasi“. Inji shi.

Gwamnan ya kuma shawarci waɗanda suka karɓi tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, musamman wajen kafa sana’o’i.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • A Yau Litinin Ce Aka Gudanar Da Sallar Edi Da Bukukuwan Sallah A Nan Iran Da Wasu Kasashen Musulmi
  • Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi
  • Eid-el-Fitr: Sarkin Kauru Ya Gargadi Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai
  •  Kasashen Iran Da Tunisya Suna Shirin Bunkasa Alaka A Fagagen Yawon Bude Ido
  • An Gudanar Da Gagarumar Zanga- Zanga Ta Ranar Qudus Ta Duniya A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • Hamas ta yi Tir da kakkausar murya da harin Isra’ila kan masu aikin ceto a Gaza
  • Adadin mamata a girgizar kasar Myanmar ya ka 1,644
  • Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu
  • Gwamnati Ta Ba da Umarnin Tafiya Yi Wa Ƙasa Hidima Ga Duk Masu HND
  • Me Ya Sa Fina-finai Masu dogon Zango A Masana’antar kannywood ke Zama Cin kwan Makauniya?