Boko Haram ta kashe sojoji 22 da mayaƙan JTF a Borno
Published: 27th, January 2025 GMT
Gomman sojoji da mayaƙan sa-kai na Sibiliyan JTF sun kwanta da dama a wata arangama da mayaƙan Boko Haram a yankin Mai-saleh da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe.
Majiyoyin tsaro sun bayyana ce ’yan na Boko Haram sun kai wa jami’an tsaron hari ne bayan da jami’an tsaron sun kwace wani babban sansaninsu da ke Mai-Saleh a tsakanin jihohin biyu.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro mai barin gado, Manjo-Janar Edward Buba, ya tabbatar da rasuwar sojoji 22 a harin.
“Jimillar sojoji 22 ne suka rasu wasu da dama sun jikkata a yayin artabun,” in ji Edward Buba. Amma wasu majiyoyi sun ce sojojin da suka kwanta dama sun haura 27.
Mace ta rasu, wasu sun jikkata yayin da nakiya ta fashe a Neja ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a KanoWani jami’in Sibiliyan JTF ya bayyana cewa maharan sun kawo musu harin ne makaman RPG da ’yan ƙunar baƙin wake da jirage marasa matuƙa wajen halaka jami’an tsaron.
Sanarwar da Majo-Janar Edward Buba ya fitar ta ce sojojin sun kashe mayaƙa na musamman na Boko Haram fiye da 70 a yayin artabun.
Ya bayyana cewa kwamandan mayaƙan mai suna Talha da takwarorinsa Abu Yazeed da Malam Umar na daga cikin waɗanda sojoji suka kashe a arangamar ta ranar Asabar.
Edward Buba ya ce sojojin sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa na ’yan ta’addan. Ya ƙara da cewa mayaƙan sun yi amfani da ’yan kunar baƙin wake da motoci dauke da abubuwan fashewa ne wajen kai harin.
Ya ce bayan samamen da sojojin suka ƙaddamar domin murƙushe ’yan ta’addan tun ranar 16 ga watan nan na Janairu, sojojin sun kashe ’yan ta’adda sama da 70 sa manyan kwamandojinsu.
Yadda abin ya faruƊaya da cikin dakarun da suka yi musayar wutar ya shaida wa wakilinmu cewa an kawo musu harin ne bayan da a kusa da wani kududdufi, bayan da suka kwace sansanin Mai-Saleh daga hannun mayaƙan Boko Haram.
“Mun kwace sansanin Mai Saleh wanda ɗaya ne daga cikin manyan sansanonin Boko Haram, amma daga bisani aka kawo mana hari a kusa da ƙoramar.
“A nan ne suka kashe mana kwamanda da sojoji 26 daga Sashe na 2 na Rundunar Operation Hadin Kai. Akwai kuma sojojin da suka jikkata,” in ji shi.
Wani jami’in Sibiliyan JTF ya ce ya rasa ɗan uwansa da abokan aikinsa biyar a yayin artabun. Ya bayyana cewa maharan sun kawo musu harin ne makaman RPG da ’yan ƙunar baƙin wake da jirage marasa matuƙa wajen halaka jami’an tsaron.
Ya ce, “gari ya yi duhu lokacin da muka isa ƙoramar, na ji ƙarar wani abu kamar jirgin yaki, sannan ƙarar fashewa.
A kan idona motar da ke gabanmu ta fashe, duk mutanen cikinta suka mutu, yana mai cewa yawan mamatan na iya ƙaruwa.
Shi ma wani soja da ta ce adadin mamatan na iya ƙaruwa, ya bayyana cewa abokan aikinsa da dama sun rasu a harin, domin “babu wanda zai iya faɗan haƙiƙanin yawan waɗanda suka rasu saboda akwai mafarauta da Sibiliyan JTF da sojoji daga Goniri, Buni Yadi, Damboa da Sabon Gari da aka yi aikin tare da su.
Daga Hamisu Kabir Matazu (Maiduguri); Sagir Kano Saleh & Idowu Isamotu (Abuja)
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Janar Sari: Sojojinmu Sun Yi Taho Mu Gama Da Amurkawa Sau 3 A Cikin Sa’o’i 24
Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sau uku su ka yi taho mu gama da sojojin da suke cikin jirgin dakon jirayen yakin Amurka “ Trauman” a cikin sa’oi 24.
A wata sanarwa da janar Yahya Sari ya yi a jiya Asabar ya bayyana cewa; Sun kai wa jirgin dakon jiragen yakin na Amurka da kuma sauran jiragen da suke ba shi kariya a cikin tekun “Red Sea”.
Kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma ce; Sun kai wa jiragen na Amuka hare-hare ne da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami mabanbanta.
An shiga makwanni na uku kenan da sojojin na Yemen suke mayar da martani akan hare-haren da sojojin Amurka da Birtaniya suke kai wa kasarsu.
Kasar ta Yemen tab akin jagororinta za su ci gaba da kai wa manufofin HKI hare-hare har zuwa lokacin da za a daina yaki da Gaza da kuma dauke takunkumin da aka akakaba wa zirin na hana shigar da kayan agaji.
Baya ga kai wa Amurka da Birtaniya da sojojin na Yemen suke yi, suna kuma hana duk wani jirgin ruwa ratsawa ta tekun “Red Sea” matukar zai nufi HKI.
Sa’o’i kadan da su ka gabata ma dai sojojin kasar ta Yemen sun harba makamai masu linzami zuwa HKI