Abin Fashewa Ya Hallaka Mutum Guda, Ya Jikkata 6 A Neja
Published: 27th, January 2025 GMT
Wani fashewa da ake zargin daga abubuwan fashewa ne da wani mai hakar zinariya ya ajiye a Sabon Pegi, ƙaramar hukumar Mashegu a Jihar Neja, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da jikkatar mutane shida a ranar Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa Yushau, wani mai haƙar haƙar zinariya, ya ajiye abubuwan fashewar ne a gida kafin su tashi yayin da ake shirya su don kai wa wuraren haƙar ma’adinai a yankin.
Kakakin Rundunar ’Yansanda ta Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar Fatima Sadauki tare da jikkatar wasu mutane shida da aka kai Asibitin Kainji domin jinya. Haka kuma, gidaje 12 sun lalace sakamakon fashewar.
Kakakin ya ƙara da cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya umurci a gudanar da bincike tare da tura tawaga ta cire abubuwan fashewa (EOD-CBRN) zuwa wurin domin bincike na musamman. Ya kuma bayyana cewa wanda ya ajiye abubuwan fashewar, Yushau tuni ya tsere, amma an tabbatar da zaman lafiya a yankin yayin da ake ci gaba da sa ido.
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Nada Jami’an Alhazai 27 Tare Da Kara Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajji
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce Gwamna Umar Namadi ya amince da nadin sabbin jami’an cibiyoyi 27 da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Babban Daraktan Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
Ya ce, an zabo sabbin jami’an cibiyar ne daga dukkan kananan hukumomin jihar 27, kuma za su samu horo da jagoranci kan ayyukan da hukumar ta dora musu.
Ya kuma bayyana cewa, tuni hukumar ta gudanar ta taron bita ga dukkan jami’an shiyyar da nufin sanar da jami’an irin ci gaban da aka samu a shirye-shiryen gudanar da aikin hajji mai zuwa.
Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da gudanar da harkokin ilimantar da Alhazan game da aikin hajjin.
Ya yi bayanin cewa, an tanadar da zababbun malaman addinin Islama domin gudanar da aikin bita ga Alhazai da ke gudana a babban masallacin Dutse.
Ya ce, hukumar jin dadin Alhazai ta jihar ta bullo da sabbin dabaru na ilmantar da Alhazan na bana.
Ya shawarci maniyyata musamman wadanda wannan ne Hajjinsu na farko, da su yi amfani da wannan dama wajen inganta iliminsu na addini da sauran muhimman bayanai da za su taimaka musu wajen gudanar da aikin hajji karbabbe.
Shugaban ya ce, nan ba da jimawa ba za a rufe gudanar da taro bitar har sai bayan watan Ramadan.
Ya ce, taron bitar da hukumar ta gudanar, ya bai wa maniyyatan jihar damar samun ilimin aikin hajji da kuma sanin tsare-tsaren da hukumomin Saudiyya da hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON suka tanadar a aikin hajjin bana.
Don haka, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yaba wa mahalarta taron bitar, inda ya kara da cewa hakan karin ilimi ne da zai amfane su baki daya.
Da yake tsokaci game da rajistar da ake ci gaba da yi a jihar, shugaban hukumar ya yi kira ga maniyyatan da suka fito daga dukkan kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar da har yanzu ba su kammala biyan kudin ba, su yi kokarin cikawa domin hukumar NAHCON ta kara wa’adin biyan kudin zuwa mako mai zuwa.
Labbo, ya ce ranar wa’adin zai cika ne a ranar 7 ga watan Maris 2025, inda ya kara da cewa, hukumar ta biya kusan Naira biliyan 6 ga NAHCON.
Ya kuma yabawa jami’an shiyyar da suka yi rijista, tare da tattara kudaden ajiyar hajji a yankunansu.
Shugaban hukumar, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewa da sabbin jami’an cibiyar da kuma goyon baya da hadin kai da ake ba hukumar a kowane lokaci.
Usman Muhammad Zaria