NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Hanyar Intanet
Published: 27th, January 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ci-gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci.
A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da ɓangarori da dama.
Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka koma intanet da kasuwancinsu.
Shrin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ƙalubale da ke tattare da wannan harka, da damar da ake samu idan an rungume ta, da kuma dabarun yin nasara a cikinta.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kasuwanci yanar gizo
এছাড়াও পড়ুন:
An Watsa Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Karon Farko A Najeriya
A ranar 25 ga wata, agogon Najeriya, ofishin karamar jakadiya kasar Sin dake Legas, da tawagar Sinawa wadanda ke kasar, sun gudanar da jerin ayyuka don yin maraba da murnar bikin Bazara na shekarar maciji bisa kalandar gargajiyar Sinawa. An gudanar da bikin nune-nunen abinci, da nune-nunen kayayyaki, da liyafar maraba bi da bi, wanda ya samu halartar mutane sama da 2,000 da suka hada da Sinawa dake kasar da abokai ‘yan Najeriya.
Kafin an fara liyafar a maraice, an watsa bidiyon dandanon shagalin murnar bikin Bazara na shekarar maciji na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, Kyan hoton bidiyon mai kayatarwa kuma mai cike da ma’anar kimiyya da fasaha ya matukar burge bakin da ke wurin, ya kuma tada sha’awa mai karfi na yawancin baki ‘yan Najeriya, masu kallo sun kalli bidiyon a tsanake kuma sun yi kyakkyawar tafawa ma bidiyon. (Mohammed Yahaya)