Jagoran Kungiyar Ansarullah Ta Yemen Ya Shirin Na Tunkarar Harin Amurka
Published: 27th, January 2025 GMT
Jagoran kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wani harin Amurka kuma ya gargadin sojojin haya
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya tabbatar da cewa: Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta wajen tallafawa haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kokarin murkushe al’ummar Falasdinu, yana mai jaddada tsayin daka da matsayarsa da ke tafiya a kan tubalin gaskiya, ikhlasi da ke gudana a tsakanin al’ummar Falastinu da ‘yan gwagwarmayarsu.
Sayyid Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya bayyana a yayin zagayowar ranar shahadar Sayyid Hussein Badruddeen al-Houthi, cewa: Abin da hukumomi suka yi a shekara ta 2004 kan shahidi wanda shi ne ya kafa tattakin Alkur’ani, kuma shugaba shahidi Hussein Adwan, ba a yi adalci ba, yana mai nuni da cewa abin da shahidin Alkur’ani ya yi shi ne koyar da tarbiyyar Alkur’ani, da kalubalantar masu girman kai da kuma kauracewa kayayyakin Amurka da Haramtaciyyar kasar Isra’il kan matakin da suka dauka na kaddamar da hare-haren wuce gona kan al’ummar kasarsu.
Ya kara da cewa, bayan abubuwan da suka faru a ranar 11 ga watan Satumba, Amurka ta yi shirin mayar da ita tamkar wata kafa ta wani gagarumin yakin neman zabe na tsaurara iko a kan al’ummar kasar, da mamaye yankunanta da kuma kawar da asalinta, ya ci gaba da cewa gwamnatocin da suka mika wuya ga Amurka kuma an bude dukkan kofofin zuwa gare ta, ciki har da gwamnatin Yemen a karkashin taken kawancen yaki da ta’addanci, inda gwamnati a Yemen bayan a abubuwan da suka faru na ranar 11 ga watan Satumba suka bude hanya ga Amurka a cikin soja, tsaro, tattalin arziki, ilimi, kafofin watsa labaru da kuma maganganun addini.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%.
Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo babban yankin kasar a bara ya kai miliyan 131.9, wanda ya karu da kaso 60.8%, kuma daga cikinsu miliyan 26.94 ’yan kasashen waje ne, sauran kuma sun fito daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan, kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe ya kai dala biliyan 94.2, wanda ya karu da kaso 77.8%. Ban da haka, yawan mazauna babban yankin kasar Sin da suka fita daga kasar ya kai miliyan 145.89, kuma daga cikinsu miliyan 97.12 sun je yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp