Rundunar Sojin Najeriya ta 8 da ke Sokoto ta bayyana ayyukanta na zamantakewar jama’a na yammacin Afirka WASA, a matsayin muhimmin kayan aiki don wanzar da hadin kai da ci gaba a yankin yammacin Afirka.

 

Babban Kwamandan Rundunar, Manjo Janar Ibikunle Ajose ya bayyana haka a wajen taron na bana da aka gudanar a Bataliya ta 26 dake jihar Sokoto.

 

Ajose ya ce hukumar ta WASA tana baiwa hafsoshi da sojoji da iyalansu damar yin mu’amala cikin yanayi mai kyau.

 

Ya bayyana cewa, tarihin wannan biki ya samo asali ne tun a shekarar 1901, a lokacin shigar da Najeriya cikin rundunar sojojin kasashen yammacin Afrika, saboda al’adu daban-daban na sojojin kasashen yammacin Afirka, shi yasa mahukunta a wancan lokaci suka gabatar da WASA duk shekara domin sojoji su shiga.

 

Kwamandan ya yi nuni da cewa zaman lafiya da hadin kai da ake samu a cikin sojojin Najeriya sakamakon manufofin WASA ne a yankin yammacin Afirka.

 

Manjo Janar Ibikunle Ajose ya kuma duba irin nasarorin da rundunar ta samu kan yaki da ‘yan bindiga da sauran tashe-tashen hankula da ke faruwa a yankin Arewa maso Yamma .

 

Ya ce, a shekarar 2024, rundunar ta samu nasarar gudanar da ayyukanta na yaki da ayyukan bata gari a duk fadin Nijeriya.

 

Ya ce nasarorin da aka samu sun hada da kaddamar da runduna ta 248 ta Recce a Illelah, da tura babban hafsan soji na musamman na Bataliya ta 7 a karamar hukumar Gudu a jihar Sokoto da kaddamar da sabbin kayan aiki na sojojin sama da sauran makaman yaki a Sokoto.

 

A cewarsa, abubuwan da suka faru sun haifar da nasarori da dama a ayyukan sojoji na fadin yanki na 8.

 

A nasa jawabin, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin sana’o’i da tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya, ya yabawa kokarin rundunar na ci gaba da kulla alaka mai karfi da al’adunsu.

 

Aliyu ya ce bikin ya zama abin tunatarwa ne kan alhakin da ya rataya a wuyansu na bunkasa fahimtar juna, mutunta juna, da hadin kai a tsakanin kungiyoyi da al’ummomi daban-daban a yammacin Afirka.

 

NASIR MALALI/Wababe

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: wasa yammacin Afirka

এছাড়াও পড়ুন:

 Janar Sari: Sojojinmu Sun Yi Taho Mu Gama Da Amurkawa Sau 3 A Cikin Sa’o’i 24

Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sau uku su ka yi taho mu gama da sojojin da suke cikin jirgin dakon jirayen yakin Amurka “ Trauman” a cikin sa’oi 24.

A wata sanarwa da janar Yahya Sari ya yi a jiya Asabar ya bayyana cewa; Sun kai wa jirgin dakon jiragen yakin na Amurka da kuma sauran jiragen da suke ba shi kariya a cikin tekun “Red Sea”.

Kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma ce; Sun kai wa jiragen na Amuka hare-hare ne da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami mabanbanta.

An shiga makwanni na uku kenan da sojojin na Yemen suke mayar da martani akan hare-haren da sojojin Amurka da Birtaniya suke kai wa kasarsu.

Kasar ta Yemen tab akin jagororinta za su ci gaba da kai wa manufofin HKI hare-hare har zuwa lokacin da za a daina yaki da Gaza da kuma dauke takunkumin da aka akakaba wa zirin na hana shigar da kayan agaji.

Baya ga kai wa Amurka da Birtaniya da sojojin na Yemen suke yi, suna kuma hana duk wani jirgin ruwa ratsawa ta tekun “Red Sea” matukar zai nufi HKI.

Sa’o’i kadan da su ka gabata ma dai sojojin kasar ta Yemen sun harba makamai masu linzami zuwa HKI

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi
  • Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya
  • Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano
  • Eidl Fitr: Gwamna Dauda Lawal Ya Buƙaci A Samu Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi
  •  Janar Sari: Sojojinmu Sun Yi Taho Mu Gama Da Amurkawa Sau 3 A Cikin Sa’o’i 24
  • Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
  • MDD Ta Yi Gargadi Akan Mummunan Yanayin A Sudan Ta Kudu
  • An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja
  • Iran: Ta’addancin sojojin Amurka a kan Yemen ‘barazana’ ne ga zaman lafiyar duniya