Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-31@20:08:11 GMT

Saura Kiris Mu Kai Ga Bello Turji – Rundunar Sojan Nijeriya

Published: 27th, January 2025 GMT

Saura Kiris Mu Kai Ga Bello Turji – Rundunar Sojan Nijeriya

Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya baiwa al’ummar jihar Zamfara aniyar rundunar sojojin Najeriya wajen ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

 

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau.

 

Kungiyar WASA wani taron ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin murnar dimbin al’adun gargajiya na wannan kasa mai girma.

 

Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu a cikin annashuwa don bikin da kuma nuna ƙarshen ayyukan shekara.

 

Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da ‘yan fashi daji da kuma dawo da zaman lafiya a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba daya, ya yi kira ga sojojin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa, sadaukarwarsu na da matukar muhimmanci wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

 

A cewarsa, a halin yanzu fitaccen jagoran ‘yan bindigar Bello Turji na kan hanyarsa ta zuwa lahira saboda hare-haren da sojoji ke kai wa a jihar Zamfara.

 

“Bello Turji matsoraci ne kuma ya yi watsi dadakarunsa saboda matsin lamba da muka yi masa. Mun share da yawa daga cikinsu kuma za mu ci gaba da ci gaba da kai farmakin kai tsaye zuwa maboyarsu.”

 

Kwamandan Birgediya wanda ake yi wa lakabi da “Jar Kunama”, ya yabawa al’ummar Zamfara bisa yadda suke ba da hadin kai, musamman ta hanyar samar da muhimman bayanan sirri, wanda ya haifar da gagarumar nasara.

 

Tun da farko, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Meriga ya wakilta, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa namijin kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar ta Zamfara.

 

Taron WASA na bana a Gusau ya samu halartar manyan baki da suka hada da sarakunan gargajiya da shugabannin sauran hukumomin tsaro kamar rundunar sojojin saman Najeriya da jami’an tsaro da dai sauransu.

 

Muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun hada da yawon shakatawa, baje kolin al’adu da raye-raye, wasan taekwondo, tuggun yaki, da kunna wuta da Kwamandan Brigade ya yi da dai sauransu.

 

Yayin da wasu da dama da suka yi nasara suka je gida da kyaututtuka daban-daban.

 

COV/AMINU DALHATU/Wababe

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: wasa Zamfara rundunar sojojin Najeriya zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa.

Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki.

Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah

Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan hanyoyin da mutum ya kamata ya bi don komawa cin abinci yadda ya kamata bayan azumtar watan Ramadana.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda ‘Yan Banga A Edo Suka Yi Sanadin Kashe Matafiya Mafarauta 16 – Direban Motar
  • Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi
  • NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana
  • Dan shekara 4 ya kira wa mahaifiyarsa ’yan sanda
  • Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya
  • Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano
  •  Janar Sari: Sojojinmu Sun Yi Taho Mu Gama Da Amurkawa Sau 3 A Cikin Sa’o’i 24
  • Gobe Ta Ke Sallah A Nijeriya – Sarkin Musulmi
  • Jami’an Tsaro A Jihar Kano Na Tarayyar Najeriya Sun Hana Bikin Dabar NA Sallar Bana
  • Kisan ‘Yan Arewa 16 A Jihar Edo: Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Ta Nemi Adalci