Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-01@05:20:19 GMT

Jami’ar Ahmadu Bello Ta Yaye Dalibai Fiye Da Dubu 20 a Bana

Published: 27th, January 2025 GMT

Jami’ar Ahmadu Bello Ta Yaye Dalibai Fiye Da Dubu 20 a Bana

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabiru Bala ya roki Majalisar Dokoki ta kasa da ta yi gyare-gyaren doka don ware cibiyoyin ilimi daga zama hukumomi masu samarda kudaden shiga.

 

Ya yi wannan roko ne a wajen bikin yaya=e dalibai karo na 44 da aka gudanar a dandalin Mamman Kontagora da ke Samaru a Zariya.

 

Shugaban jami’ar ya ce idan haka ta faru, jami’o’in za su mayar da hankali ne a matsayin manyan cibiyoyin kawo ci gaban kasa.

 

Ya yi nuni da cewa Jami’ar Ahmadu Bello kamar yadda jami’o’in Najeriya da dama ke fuskantar kalubalen kudi don tallafa wa manufofinta na ci gaba da zamanantar da ayyukanta.

 

Farfesa Bala ya yi magana ne game da umarnin kotun masana’antu ta kasa na a rufe asusun ajiyar jami’ar dake a babban bankin Najeriya ajiya wanda ke cike da kudi naira miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar da tamanin da biyar.

 

Ya yi nuni rashin jin dadin ganin c ewa wannan asusun jami’ar da abin ya shafa ya kunshi wasu kudade na sassan daban daban kamar tallafin bincike na gida da na waje, kudade na sassan jami’ar da ke da alaka da bincike bincike.

 

Ya bayyana cewa, a sakamakon wannan odar, dukkan ayyukan da suka shafi kashe kudi kamar su tsaftar muhalli, wutar lantarki da sauran kayayyakin masarufi na fuskantar cikas.

 

Tun da farko a nasa jawabin, shugaban jami’ar kuma shugaban majalisar gudanarwar jami’ar, Alhaji Mahmood Yayale Ahmed ya ce tsarin jami’o’in Najeriya na fuskantar kalubale da suka hada da kudade, mulki da gudanarwa.

 

Don haka ya ba da shawarar samun ‘yancin kai na kuɗi don tabbatar da cewa jami’o’i sun kasance matattarar masana da kwararri da tunani da sabbin abubuwa.

 

Shima a nasa jawabin, Uban jami’ar, Obi na Onitsha, Nnaemeka Alfred Achebe, ya dorawa daliban da suka yaye aikin yin amfani da wannan karni na 21 a matsayin shekarun juyin zamani.

 

Bikin karo na 44, an yaye dalibai 21,952 da suka kammala karatun digiri na 2023/2024, daga cikinsu 5,756 sun sami digiri na biyu yayin da 16,196 suka sami digiri na farko.

 

COV/HALIRU HAMZA/Wababe

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’an Diblomasiyyar Kasashen Rasha Da Amurka Zasu Sake Haduwa A Birnin Istambul A Gobe

Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu.

Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko.  Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau.

A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana ruwa guda a ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da Mosco.

A ranar 18 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne a karon farko tun bayan fara yakin Ukraine jami’an diblomasiyyar kasashen biyu suka hadu a birnin Riyad na kasar Saudiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwararrun Masana Sun Gargadi Kan Karkatar da Kudaden Fansho Na Biliyan ₦ 758
  • MDD Ta Bayyana Cewa Yara Fiye Da 100,000 Ne Suka Ka Yi Rijistan Fara Karatu A Makarantun Gaza Na Sabuwar Shekarar Karatu
  • Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki 
  • Gwamnatin Kano Ta Shirya Taron Bita Don Jami’an Watsa Labarai
  • Kwara ta Raba Littafai Fiye da Dubu 74 Kyauta Ga Dalibai
  • Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki
  • Sarkin Moroko Ya Buƙaci Yan Kasar Kada Su Yi Layya A Bana
  • Gwamna Namadi Ya Nada Jami’an Alhazai 27 Tare Da Kara Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajji
  • Jami’an Diblomasiyyar Kasashen Rasha Da Amurka Zasu Sake Haduwa A Birnin Istambul A Gobe
  • Jami’an tsaro sun tarwatsa zanga-zangar da ta ɓarke a Kano