Kenya Ta Sanar Da Taron Kungiyar Kasashen Gabashin Afirka, Tare Da Tshisekedi Da Kagame
Published: 27th, January 2025 GMT
Shugaban kasar Kenya William Ruto a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, zai gudanar da wani babban taro na musamman na kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC a cikin sa’o’i 48 masu zuwa tare da halartar shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi da shugaban Rwanda Paul Kagame.
Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan tawayen M23 ke ci gaba da dannawa kan birnin Goma inda ake ta musayar wuta.
A cewar wasu majiyoyin MDD da na tsaro, sojojin Rwanda da mayakan M23 sun shiga birnin a ranar Lahadi, in ji kamfanin dillancin labaran Faransa.
Yakin da ake gwabzawa a kusa da Goma da kuma harbe-harbe da aka yi a birnin ya kuma sa mazauna babban birnin lardin ketare kan iyaka zuwa kasar Rwanda.
A wani labarin kuma sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya zargi gwamnatin Kigali kan sabon fadan da akeyi a gabashin DRC.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Bikin Ranar Sojin A Iran 18 Ga Watan Afrilu Tare Da Gudanar da Fareti A Gaban Shugaban Kasar
An fara gudanar da bukukuwan ranar soji a Iran a ranar 18 ga watan Afrilu ta hanyar gudanar da faretin soja a gaban shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian
An fara faretin soji na sojojin kasar Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar sojoji ta 18 ga watan Afrilu.
A jiya Juma’a 18 ga watan Afrilu ne sojojin kasar Iran suka fara faretin soji na murnar zagayowar ranarsu da kuma irin bajintar jarumtakar sojojin kasar, a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin babban birnin kasar Tehran.
A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA na Iran, faretin ya samu halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran.
Faretin dai zai kunshi rundunonin yaki da motoci masu sulke na rundunar sojojin kasa na kasar, mayakan sojin sama, makamai da na’urorin tsaro na sojojin sama, da na’urorin sojan ruwa da ake iya jigila da su.
Haka kuma za a baje kolin wasu daga cikin nasarorin da Iran ta samu, da makamai masu linzami, na sama, da na ruwa, da kuma na kasa gami da jiragen sama marasa matuka ciki.