An Tsawaita Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila Da Lebanon Har Zuwa 18 Ga Watan Fabrairu
Published: 27th, January 2025 GMT
An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko.
An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025.
Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan.
Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon.
“Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,” in ji Mikati a cikin wata sanarwa, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Duk da haka a ranar Lahadi sojojin Isra’ila sun bude wuta kan al’ummar Lebanon da ke kokarin komawa gidajensu a kudancin kasar, inda suka kashe fararen hula akalla 22 tare da jikkata wasu fiye da 120 na daban.
‘Yan kasar ta Lebanon, sun sha alwashin komawa kauyuka da garuruwansu, duk da barazanar da Isra’ila ke yi.
A karshen mako ne, sojojin Isra’ila suka gargadi al’ummar Lebanon da kada su koma garuruwansu na kudancin kasar.
Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah a ranar 27 ga watan Nuwamban 2024, bayan ta tafka asara mai yawa a fagen daga da kuma kasa cimma burinta duk da kashe mutane sama da 4,000 a Lebanon.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yarjejeniyar tsagaita
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu
Kasashen Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu domin cin moriyar juna a matsayinsu na makobta.
Wannan bayyanin ya fito bayan tattaunawa data wakana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu a birnin Yamai bayan kwashe watanni ana takaddama.
Yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai Nijar an gudanar da wani babban taro tsakanin shugabannin diflomasiyyar kasashen biyu don sake farfado da hanyoyin hadin gwiwa a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro.
Ministan harkokin waje da hadin gwiwa na Nijar Bakary Yaou Sangaré da takwaransa na Najeriya Yusuf Maitama Tuggar sun gana a ranar 16 ga ga watan nan, lamarin dake nuni da wani gagarumin sauyi na dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da ta yi tsami tsawon watanni biyo bayan juyin mulkin da ya faru a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
bangarorin biyu sun kuma tattauna kan barazanar ta’addanci a kan iyakokinsu, inda suka jaddada aniyarsu ta hada karfi da karfe wajen yakar kungiyoyin da ke dauke da makamai da ke kawo cikas wajen aiwatar da dukkanin shirye-shiryen ci gaba a kasashen biyu cikin shekaru da dama. Inda suka bukaci ma’aikatun tsaron kasashen biyu da su ci gaba da hadin gwiwa a fannin tsaro.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna ta tabarbare ne a lokacin da Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen daukar matakan kakabawa Yamai takunkumin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta kakabawa kasar, wanda hakan ya bata dangantakar da ke tsakaninsu.