Bankin Duniya Da IMF Sun Buƙaci CBN Ya Daƙile Hauhawar Farashi A Nijeriya
Published: 27th, January 2025 GMT
Ya kuma yi gargadi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziƙi zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, in ji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.
.কীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar ‘Yansan Nijeriya Za Ta Gudanar Atisaye Ga Jami’anta a Jigawa
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.
A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da tsaron lafiyar jama’a.
Don haka rundunar ta bukaci mazauna kauyen Tsohon Kafi da kewaye da kada su firgita da jin karar harbe-harbe a yayin atisayen.
Abdullahi ya ce, za a sanya ido sosai a kan dukkan ayyukan da kuma gudanar da su a cikin yanayi mai aminci da kulawa.
Rundunar ta kuma yaba da ci gaba da goyon baya da hadin kan al’umma wajen tallafawa kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
KARSHE/USMAN MZ