‘Yan Bindiga Sun Sace Magidanci Da Iyalansa Da Makwabta A Abuja
Published: 27th, January 2025 GMT
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum da matarsa da dansa da wasu mutane biyu a Bwari da ke babban birnin tarayya, Abuja (FCT). LEADERSHIP ta tattaro cewa, an kai harin ne a unguwar Chikakore da ke Kubwa da misalin karfe 12 na safiyar ranar Litinin. Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon Tinubu Ya Isa Tanzania Don Halartar Taron Makon Makamashi Na Afrika Majiyoyi sun ce, kimanin mahara 30 ne dauke da bindigogi kirar AK-47, suka kai hari gidan wani Mista Adefija Michael Akinropo, inda suka yi awon gaba da shi, da matarsa, da dansa, da kuma kanensa.
এছাড়াও পড়ুন:
Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe
Wani mummunan al’amari ya girgiza al’umma a Ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, inda ake zargin wani magidanci ya jagoranci sacewa da kashe ɗansa mai shekara shida domin yin tsafin kuɗi.
Ana zargin cewa mahaifin yaron shi ne jagoran kisan kuma Yana cikin waɗanda suka tsere, a yayin da hukumomi ke ci gaba da farautar sa.
Tuni ’yan sanda suka cafke mutane takwas bisa zargin wannan aika-aika a unguwar Bura-Bunga da ke ƙaramar hukumar.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya sanar cewa waɗanda suka shiga hannu sun amsa cewa sun kashe yaron ne bisa umarnin bokaye da suka nemi sassan jikin ɗan Adam don yin tsafin kuɗi.
An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a NasarawaBincike ya nuna wani mai shekaru 45, wanda ake zargin shi ne shugaban gungun, ya hallaka yaron tare da raba sassan jikinsa gida biyu.
Ɓangaren sama na jikinsa an jefa shi cikin rijiyar, yayin da ɓangaren kasa aka bai wa abokan laifinsa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu bokaye biyu ne suka nemi sassan jikin yaron, kuma wani matashi mai shekaru 18 ne ya sace yaron, sannan wani ya haɗa bokayen da su.
Kwamishinan ’yan sanda, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa za a tabbatar an gurfanar da duk masu hannu a wannan mummunan kisa a gaban ƙuliya.
Ya kuma yi kira ga jama’a su riƙa sa ido tare da bayar da rahoto kan duk wani abu mai kama da waɗanda ake nema jami’an tsaro.
Rundunar ’yan sanda ta jaddada aniyarta na kawo ƙarshen irin waɗannan munanan laifuka a faɗin jihar ta Gombe.