Lebanon: Mutanen Kudancin Lebanon Suna Ci Gaba Da Kowama Garuruwansu
Published: 27th, January 2025 GMT
A rana ta biyu a jere, mutanen kudancin Lebanon suna ci gaba da komawa gururwansu da kauyukansu duk da hare-haren da Isra’ila take kai musu.
Tashar talabijin din “almayadin” mai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta ce, jirgin Isra’ila maras matuki,ya jefa bom din sauti na tsorata mutanen da suke komawa garuruwan nasu ,musamman a gefen garin Lamisul-Jabal, domin hana su shiga.
Mutanen garin sun ce za su shiga garin nasu ko da kuwa za su yi shahada ko kuma su jikkata.
Haka nan kuma sojojin na HKI sun kai farmaki akan sojojin Lebanon da suka taru a yankin al-Mafilah.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa, mutane biyu sun jikkata sanadiyyar hare-haren na HKI a yau Litinin.
A jiya Lahadi ne dai wa’adin kwanaki 60 daga kare yakin Lebanon ya cika, da yarjejeniyarsa ta kunshi ficewar sojojin HKI daga garuruwan da su ka yi kutse.
Sai dai sojojin na mamaya sun ki ficewa, da hakan ya sa mutanen kudancin Lebanon su ka kutsa cikin garuruwan nasu. A kalla mutane 22 ne su ka yi shahada a jiya da kuma jikkata wasu masu yawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane Biyu Sun Mutu, 20 Sun Jikkata A Yamutsin Filin Idi A Gombe
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp