Kungiyar “ISWAP” Ta Kashe Sojojin Najeriya 20
Published: 27th, January 2025 GMT
A kalla sojojin Najeriya 20 ne su ka kwanta dama daga cikinsu har da kwamanda a wani hari da ake dangantawa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP.
‘Yan ta’addar sun kai harin ne dai a ranar Juma’ar da ta gabata a kan sansanin bataliya ta 146 dake Malam-Fatori a akan iyakar Najeriya da Nijar a jihar Borno.
Wani soja da ya tsira daga wannan harin ya fadi cewa harin ‘yan ta’addar ya dauki sa’oi 3, kuma sun je wurin ne a cikin manyan motoci tare da shammatar sojojin.
Kamfanin dillancin labarun Reuters wanda ya ambato sojan ya ce, maharan sun rika harbinsu ta kowace kusurwa, sai dai sun mayar da wuta.Haka nan kuma ya tabbatar da cewa an kashe kwamandnsu.
Mazaunan yankin da aka kai harin sun tabbatar da cewa maharan sun kone gine-gine masu yawa, da ya tilastawa mazauna yankin yin hijira.
Haka nan kuma an tabbatar da cewa har zuwa Asabar da dare an rika ganin maharan a cikin wannan yankin suka karakaina.
Ita dai kungiyar “ISWAP” ta balle ne daga Bokoharam a 2016, kuma tana kai wa sojoji da jami’an tsaron Najeriya hare-hare. A tsawon shekaru 15 na hare-haren ‘yan ta’adda a wannan yankin mutane kusan 40,000 ne su ka kwanta dama,wasu miliyan biyu kuwa su ka tarwatse.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta yi tir da matakin Isra’ila na shirin takura masu ibada a masallacin Quds
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi ishara da umarnin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayar na ba wa masu ibada 10,000 kawai damar gudanar da sallar Juma’a a harabar masallacin Al-Aqsa, tana mai cewa matakin wani lamari ne mai matukar hadari da ke da nufin tauye ‘yancin addini.
Hamas ta ce, umarnin ‘yan sandan Haramtacciyar Kasar Isra’ila cin zarafi ne ga dukkan ka’idoji, yarjejeniyoyin da kuma dokoki na kasa da kasa, sannan kuma hakan tsokana ce kai tsaye ga musulmi.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, irin wadannan tsare-tsare ba za su yi tasiri wajen sauya asali da tarihin masallacin Al-Aqsa ba.
Bugu da kari kuma Hamas ta dora alhakin abin da hakan zai iya haifarwa a kan gwamnatin yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayin kin musulunci.
Daga karshe kungiyar Hamas ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kasashen duniya da su dauki tsauraran matakai domin dakile wannan mataki na keta alfarmar masallacin Al-Aqsa, da kuma tabbatar da cewa al’ummar Palastinu na gudanar da ibadarsu cikin ‘yanci.