Kungiyar M23 Ta Sanar Da Kwace Iko Da Garin Goma
Published: 27th, January 2025 GMT
Ana ci gaba da fada mai tsanani a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo tsakanin sojojin gwamnati da kuma mayakan kungiyar M 23 da suke samun goyon bayan kasar Rwanda.
A yau Litinin wannan kungiyar ta sanar da cewa ta kama garin Goma da shi ne babban birnin yankin gabashin kasar ta DRC.
Wannan sanarwar dai ta zo ne gabanin cikar wa’adin sa’oi 48 da kungiyar ta bai wa sojojin gwamnatin DRC da su a jiye makamansu a kasa.
MDD ta bayyana cewa da akwai rudani a tsakanin mutanen garin da adadinsu ya kai miliyan biyu.
Da akwai dubban mutanen yankin da su ka sami mafaka a cikin garin na Goma saboda yakin da ake fama da shi.
‘Yan tawayen sun yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankulansu,tare da yin kira ga sojojin gwamnati da suke cikin garin da su kai kansu cikin filin wasan kwallo kafa na birnin.
Gwamantin kasar ta bayyana abinda M23 ta yi da cewa shelanta yaki ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar ECOWAS Ta Fice Daga Guinea-Bissau Bayan Barazana Daga Shugaban Kasar
Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar.
A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.”
Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa.
ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci.
Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.
Amma daga bisanio ya zarge su da wuce gona da iri ta hanyar tattaunawa da wasu shugabannin ‘yan adawa.
Ita dai tawagar ta ECOWAS, an dora mata alhakin samar da mafita ta samar da zaman lafiya a kasar Guinea-Bissau, ta hanyar mai da hankali kan cimma matsaya ta siyasa kafin zaben da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Nuwamba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Umaro Sissoco Embalo ke shiga takun tsaka da tawagar ECOWAS a kasar sa ba. A lokacin da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa tare da goyon bayan jami’an tsaro, ya kori mambobin ECOWAS da ke kasar tare da tare da cewa bai maraba da wakilin kungiyar.