Xi Ya Aike Da Katin Murnar Sabuwar Shekarar Al’ummar Sinawa Ga Abokansa A Jihar Iowa Ta Amurka
Published: 27th, January 2025 GMT
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan hulda da aminai.
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe
Ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta janye binciken sashe na 232 kan shigo da jan karfe kasarta, inda ta bayyana cewa, zargin da ake yi na cewa kasar Sin na amfani da tallafin gwamnati da karfin samar da hajoji fiye da kima don gurgunta abokan takara kwata-kwata ba ya da tushe.
Kakakin ma’aikatar He Yadong ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a lokacin da yake amsa tambaya kan matakin da Amurka ta dauka na kaddamar da binciken sashe na 232 kan jan karfe da aka shigar da su kasar daga kasashen waje.
Ya kara da cewa, binciken na Amurka wani aiki ne na kashin kai da kariyar cinikayya wanda ta yi bisa fakewa da “tsaron kasa”, kuma matakin zai kara yin illa ga tsarin cinikayyar bangarori daban daban da kuma kawo cikas ga daidaiton tsarin samarwa, da rarraba hajoji tsakanin sassan kasa da kasa.
Kakakin ya ce, idan Amurka ta nace kan sanya karin haraji da sauran matakan takaitawa, Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kiyaye hakkoki da moriyarta. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp