Da kuɗin hayar gidana da ke Kaduna nake sayen abinci a yanzu — Buhari
Published: 27th, January 2025 GMT
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin sayen abinci.
Buhari ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Katsina.
Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba.
“Nijeriya ƙasa ce mai wuyar sha’ani ta fuskar jagoranci amma galibin ’yan ƙasar ba su fahimci hakan ba.
“Ba za a taɓa fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke cikin riƙo da akalar jagoranci ba da ma ita kanta Ƙasa Nijeriya sai mutum ya tsinci kansa a kan madafan iko.
“A yanzu na ƙara kyan gani da lafiya fiye da yadda nake a lokacin ina Fadar Gwamnatin Nijeriya.
“Duk wanda ya ganni a yanzu zai ce na samu lafiya fiye da yadda nake a lokacin ina shugabancin Nijeriya.
“Duk da cewa na shafe shekaru takwas a matsayin Shugaban Ƙasa, amma gidaje uku kacal na mallaka — ɗaya a Daura, sai guda biyu a Kaduna.
“A yanzu na bayar da hayar ɗaya daga cikin gidajen da ke Kaduna ina samun kuɗin sayen abinci,” a cewar Buhari.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kaduna Muhammadu Buhari
এছাড়াও পড়ুন:
Babu wanda ya hana Shettima shiga Aso Rock ba— Fadar Shugaban Ƙasa
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da karaɗe kafofin sada zumunta cewa sojoji sun hana mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shiga Fadar Shugaban Ƙasa.
Labarin da ya tayar da ƙura cewa sojojin sun tare ƙofar shiga fadar shugaban ƙasa da cewa umarni ne daga sama ya koma gidansa da ke makwabtaka da fadar shugaban kasa, zuwa lokacin da Shugaba Tinubu ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai ƙasar Faransa.
Wata sanarwa da Stanley Nkwocha, hadimin shugaban ƙasa kan yada labarai, ya fitar, ta ce, babu kashin gaskiya a labarin.
Sanarwar ta kara da cewa hasali ma, masu yaɗa labarin karya sun ƙirƙirar shi ne da nufin haddasa saɓani tsakanin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin nasa.