Na’im Kassim Ya Dora Wa Amurka da Faransa da MDD alhakin Abinda Zai Faru Idan Isra’ila Ba Ta Janye Daga Labanon Ba
Published: 27th, January 2025 GMT
Abinda Ya Faru A Lebanon Nasara Ce Akan Isra’ila
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi na farko bayan cikar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki da HKI.
A jawabin nasa sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa a lokuta da dama sun yi tunanin mayar da martani akan keta tsagaita wutar yaki, sai dai an bukace su da su dakata, domin bayar damar a dauki wasu matakai na daban.
Sheikh Na’im Kassim ya zargi Amurka da rashin daukar mataki akan HKI ta dakatar da keta yarjejeniyar da take yi, duk da cewa tana cikin masu sa ido akan tsagaita wutar.
Haka nan kuma ya yi ishara da komawar mutanen kudancin Lebanon zuwa garuruwa da gidajenu duk da harbinsu da sojojin mamaya suke yi.
Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, wanda duk yake da karama yake kuma jin daukaka a tare da shi, babu abinda zai tsorata shi, da hakan shi ne abinda ya faru.
Sheikh Na’ima ya kuma jinjinawa mahukuntan kasar Lebanon akan kin amincewa da bukatar Amurka na bar wa HKI damar kara tsawon wa’adin zamansu a kudancin Lebanon. Haka kuma ya dorawa Amurka da Faransa da MDD alhakin abinda zai biyo baya idan Isra’ilan ba ta janye ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Sheikh Na im Kassim ya
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Sin: Dole Ne A Aiwatar Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da aikin soji a yammacin gabar kogin Jordan.
Fu Cong ya bayyana cewa, dole ne mulkin Gaza bayan yakin ya bi ka’idar “Falasdinawa su yi mulkin Falasdinu”, kuma ya kamata kasashen duniya su ba da goyon baya ga sake gina Gaza. Kana kasar Sin ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da su kara himma wajen kira ga samar da mafita ta siyasa ta kafa kasashe biyu da kuma ba da tabbacin da ya dace da hakan. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp