Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan Bin Ali (s) -8
Published: 27th, January 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi.
///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), sannan dan Fatimah(a) diyar manzon All..(s) na farko.
A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo mun kawo masu sauran hadisan da aka karbo daga manzon All..(s) wadanda suke magana a kan matsayin iyalan giidansa, musamman Alhassan da Alhussain(a) wajen jagorancin al-ummarsa zuwa tudun tsira. Kuma rashin binsu dai dai ne da jefa al-umma zuwa wutan jahannama.
Munji Hadisin dan Abbas wanda ya nakalto manzon All..(s) yana cewa kamar yadda taurara suka sama shiriya ga matafi daga bacewa , haka yake, iyalan gidansa, amince ne ga al-ummarsa daga bata.
Ko kuma inda yake kwatantasu da jirgin Annabi Nuhu (s), wanda ya shiga jirgin ya tsira wanda kuma ya ki shiga dai dai ne da wanda yace zai hau dutse yak are shi daga nutsewa a cikin ruwa.
Daga karshe mun ji hadisin zai dan Arkam, wanda yake magana kan cewa, manzon All…(s) ya barwa al-ummarsa nauyaya guda biyu, littafin All..da kuma iyalan gidansa, wadanda ba zasu rabuba har zuwa tabkin al-kauthara.
Manzon All..(s) ya kwatanta iyalan gidansa a shiriyarsu, kamar Alkur’ani, kamar yadda alkur’ani mai tsarki ne suma masu tsarki ne, alkur’ani maganar All..Ce suma basa sabawa All..T.
Sannan munji yadda Sayyid sharafuddeen almusawi ya fassara hadisan kwatantasu da jirgin annabi Nuhu (a) shi ne kamar Haka, wanda ya bi iyalan gidan manzon All..(s) kamar wanda ya shiga jirgin annabi Nuhu ne a lokacin Dufana, sannan wanda yak i binsu dai dai yake da wanda yaki shiga jirgin annabi nuhu, ko kuma yace zan hau dutse ya kubutar da ni daga halaka ne.
Sannan sai a ce masa kamar yadda aka fadawa wanda yake son samun tsira daga halaka a ruwan dufana, da hawa kan dutse, shi ne a ci masa, ma mai tsara a yau daga al-marain All..
A wani hadisi Abuzar Algiffari yana fada a lokacinda yake rike da kufar dakin Kaaba, yace: Ya ku mutane wanda ya sanni ya sanni, wanda bai sanni ba, nine Abuzar Algifari, naji manzon All..(s) yana cewa : kwatankwacin iyalan gidana, kamar jirgin annabi Nuhu, wanda ya shi ya tsira wanda yak i shi zai halaka.
Hadisan da dama sun zo dangane da wannan hadin na kwatanta ayalan gidana da jirgin annabi Nuhu.
A wani hadisan manzon All..(s) yana cewa sanin Ali Muhammad kubutane daga wuta. Son ali muhammadin ketarewa kan siradi ne. Kuma jibantan al-amarin iyalan ali muhammad kubuta ne daga azaba.
A wani hadisin manzon All..(s) yana cewa :” wanda ya mutu saboda son Ali muhammadin ya mutu shahidi. Ku saurara ! wanda ya mutu saboda Ali Muhammadin ya mutu wanda aka gafarta masa zunubbansa. Ku saurarar wanda ya mutu a kan son Ali muhammadin ya mutu wanda aka karbi tubansa.
Ku saurara wanda ya mutu kan son A;i Muhammadin ya mutu ta nutu mumini wanda imaninsa ya cika. Ku saurara wanda ya mutu a kan son Ali muhammad mala’ikan mutuwa zai yi masa bushara da aljanna, sannan munkari da nakira ma zasu yi masa bushara da aljanna.
Ku saurara ! wanda ya mutu yana son Ali Muhammad za’a dauki shi kamar yadda Amrya take zuwa gidan mijinta, a kai shi aljanna. Ku saurara wanda ya mutu a kan Ali Muhammadin za’a bude masa kofofi 2 a kabarinsa daga aljanna. Ku saurar duk wanda ya mutu saboda son Ali Muhammadin All..zai sanya kabarinsa wajen ziyarar mala’ikun rahamah.
Ku saurara ! wanda ya mutu a kan son iyalan gidan Muhammadu ya mutu ya mutu a kan sunna da kuma Jama’a.
Ku saurara, duk wanda ya mutu a kan kin Ai Muhammad za’a rubuta a kan goshinsa a ranar kiyama: Wanda ya debe kauna da samun rahamar All..
A wani hadisin manzon All..(s) Ku sanya iyalan gidana kamar yadda kai yake da jiki. Kamar yadda idanu suke da kai. Kai ba zai dai-daita bas ai da idanu.
Don haka wajibi ne ga musulmi su sanya Ali Muhammad kamar yadda kai yake da jiki.
Matsayin idadu ga kai, su rike shiriyarsu, su riki ayyukansu da maganganunsa, da sun yi haka da sun zama shuwagabannin sauran al-ummu, sannan masu shiryatar da sauran mutane. Sai dai sun kafa kiyayya a garesu. Sun hanasu matsayinsu, sun kaudasu daga matsayinsu…. Har zuwa inda yake cewa Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
A wani hadisin manzon All..(s) yana cewa: Mutum ba zai gushe a matsayinsa ba, a ranar kiyama sai an tambaye shi kan abubuwa 4. Daga rayuwarsa kan abinda yak arar da shi a kai. Daga daga jikinsa kan abinda ya tsofar da shi. Daga dukiyarsa kan abinda ya kashesu a kai. Daga kuma in aya samesu. Da kuma dangane da sommu ahlul baiti.
Wadannan hadisan gaba daya suna magana kan son iyalan manzon All..(s). za’a tambayesu daga nau’oiin sunsu da kuma riko da zancensu da kuma biyayya a garesu.
A wani hadisin manzon All..: Duk wanda yake jin dadin ya rayu irin rayuwata, ya kuma mutu irin mutuwata, ya kuma shiga aljanna adnin, wanda ubangijina ya shukata, to ya bi Aliyu a baya na. Kuma ya bi waliyinsa (wasiyyins) , kuma lalle ya bi iyalan gidana, a baya na, don lalle su zurriyata ne. An haliccesu daga kasan da aka halicce ni, an kuma arzutasu da fahintata da kuma ilmi na, halaka ta tabbata ga wanda ya karyata falalarsu a cikin al-ummata. Wadanda suka katse zumunci da ni ta bangarensu. All.. kada ya basu shetona .
A halin yanzu zamu takaita da wadannan hadisan wadanda aka karbo daga manzon All..(s) dangane da iyalan gidansa, saboda suna dayawa. Idan munce zmu kawosu, duk , wannan shirin yayi mana kadan.
Wannan shi ne matsayin Imam Alhassan (a), daya daga cikin iyalan gidan manzon All..(s). wasu da dama daga cikin sahabban manzon All..Suna girmamashi da kaninsa Imam Hussain(a).
Wasu daga cikin sahabban manzon All..Suna ragengento wajen yin khidima a garesu. Ga malamin wannan al-umma a cikin sahabban manzon All..(s) Ibnu Abbas idan y aga Immam Hassan (a) ya hau doki yakan yi gaggawa ya rike linzaminsa, kuma kuma dai-daita masa rigarsa sai ya zauna kan dokin kamar yadda ya dace.
Wani sahabi da ake kira Madariku dan Ziyad ya aibata Ibn Abbas kan khidimar da yakewa Imam Alhassan da Alhussain (a). sai yai banza da shi, sannan yace masa.
: Ya kai mai mummunan hali, shin ka san su waye wadannan? Wadannan sune, yayan manzon All..(s). shin baka san cewa ni’imar All..ce a gare ni, in rike masu ragamar abin hawansu ba, in dai daita masu kayansu ba.?
Musulmi suna girmamasu, har ya kaiga, a lokacinda suke zuwa aikin hajji da kafa, sai duk wata ayarin mahajjata da suka hadu da su , sais un sauka daga ababen hawansu, su taka da kafa har sais un wucesu.
Idan sun fara dawafi mutanen sun kan bude masu, sannan sukan yi cicirindo suna masa sallama suna gaidasu.
Idan abu huraina ya ga Imam Hassan (s) yakan tashi tsaye ya gaida shi ya kuma subance shi, don yaga manzon All..(s).
Don haka yakamata, ko kuma ya wajaba ga musulmi su girmama jikokin manzonsu (s), su kuma ajiyesu matsayin da Al…da manzonsa suka ajiye su.
Imam Hassan (a) ya kasance ya gudanar da wani bangare na farkon rayuwarsa tare da kakaknsa manzon All..(s). A wasu lokutan yakan fita tare da kakaknsa manzon All..(s), suna tafiya da kafa suna takawa, sai ya ga sahabban manzon All..(s) suna tashi tsaye suna girmamasu. Yana ganin yadda manzon All..(s) yake samun nasara a yake yaki masu yawa, Ya ga yadda musulmi basu da karfi amma All..T yayi ta basu nasara a kan mikiyansa makiyan manzonsa (s). Daga karshe yana da wayonsa aka bude birnin Makka, birnin mafi girma a kasashen larabawa a lokacin dukkan shuwagabannin kuraishawa suka mika kai ga jagorancinsa, sannan y aga yadda addinin musulunci ya yadu, mutane suka fara shiga addinin kungiya-kungiya kamar yadda Alkuir’ani mai girma ya shifanta lokacin.
Sannan a hankali a hankali, addinin musulunci ya kammala, manzon All..(s) ya fara tsufa, sannan wahiyi ya sauko masa yana fada masa cewa (Lalle kai mai mutuwa ne kuma suma zasu mutu)
Wannan ayar kur’ani ce, musulmi sun fahinci hakan, kuma lolacin yana fadar cewa (ina ma na san yaushe ne hakan zai faru? ) sai daga baya suratun Nasr ta sauka. Wacce itama wata manuniya ce ta cewa ya kusan barin nan duniya.
A lokacinda wannan surar ta sauka ya kasance yana yin shiru tsakanin kabbarar harama da karatun sura, sai yace . Subhanallahi wa bi hamdihi, astikfirullaha wa atubu ilaihi.
Daga nan musulmi suka fara jin tsoron cewa sun kusan rabuwa da manzon All..(s). Sannan shi kuma ya fada masu cewa (hakika an, yi mani ishara da mutuwata ta kusa).
Sannan a wancan shekara aka sauko masa alkur’ani har sau biyu. Wannan m awata alama ce.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: A wani hadisin manzon All wanda ya mutu a kan Muhammadin ya mutu iyalan gidansa iyalan gidan kamar yadda
এছাড়াও পড়ুন:
Abubuwan Da Suka Ta Da Kura A Litttafin Janar Babangida
Har ila yau, a cewarsa; Abiola ya samu mafi yawan kuri’u tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata, domin zama shugaban kasa. “Babu tantama a zuciyata, Abiola ne ya lashe wannan zabe tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata”, in ji IBB.
Kazalika, ya kuma bayyana farin cikinsa; kan yadda Buhari ya karrama Abiola da lambar yabo mafi girma ta GCFR, wadda ake bai wa shugabannin kasa.
“Ko shakka babu, Mashood Abiola shi ne ya lashe zaben shugaban kasa a 1993, da kuri’u sama da miliyan takwas a jam’iyyasa ta SDP, inda ya samu nasara a kan abokin karawarsa, Alhaji Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC”, in ji Babangida.
A jawabinsa na godiya, IBB ya bayyana rushe zaben 1993 a matsayin wani abu da ya yi yake kuma da-na-sanin yin sa a rayuwarsa.
Har ila yau, Janar Babangida a cikin littafin nasa, ya bayyana dalilinsa na kifar da gwamnatin Buhari, duk kuwa da cewa; shi ne babban hafsan sojin kasar a 1985.
Guda daga cikin dalilan nasa su ne, a babi na shida ya bayar da hujjar cewa; juyin mulkin, wani martani ne ga korafe-korafen ‘yan Nijeriya na bakar azaba da wahalar da suka sha da kuma tabarbarewar al’amuran kasar baki-daya.
“A farkon shekarar 1985, ‘yan Nijeriya sun fara fargaba game da makomar kasarmu, wanda al’amuran suka kasance a matsayin masu matukar hadari, wanda kuma hakan yanzu ma alamu ne a fili na irin wancan hatsari.
“Babu shakka, a bayyane yake ga shugabancin sojoji cewa, aikin da muka yi da nufin ceto kasarmu a shekarar 1983 ya tarwatshe”, kamar yadda ya rubuta a littafin.
Ya kara da cewa, rashin daukar mataki zai iya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin sojoji, wanda a ganinsa; hakan kan iya haifar da mummunar illa ga kasar.
“Idan sojoji suka samu rarrabuwar kai, al’ummar kasa za su bi sahunsu; sannan abin da zai biyo baya na iya kasancewa mai matukar ban tsoro da ba a taba tunani ba”, a cewarsa.
IBB, ya ci gaba da bayyana cewa, a shekarar 1983; sojoji sun hambarar da gwamnatin Shehu Shagari ne cikin hadin kai, amma sai aka fara samun rarrabuwar kawuna a tsakaninsu daga bisani.
“A matsayin sojoji na wadanda aka sani da hadin kai, sai ga shi kuma an fara samun guna-guni a tsakaninsu, wannan ne yasa dole a yi wani abu, don gudun kada mu rasa kasar”.
Babangida ya ce, “Babban abin da na ji tsoro shi ne, samun rarrabuwar kawuna da ra’ayoyi a tsakanin sojoji na iya haifar da bangaranci a tsakaninsu, wanda idan kuma aka bari abin ya ci gaba da samun gindin zama, akwai hatsarin gaske”.
Haka zalika, ya zargi Buhari da mataimakinsa Birgediya Janar Tunde Idiagbon da mayar da sojoji saniyar ware tare kuma da daukar tsauraran matakan kama-karya wajen tafiyar da mulki.
A cewar tasa, gwamnatin Buhari ta yi mulki ta hanyar tsoratarwa, maimakon sanya kyawawan fata a zukatan al’umma.
“Kyautuwa ya yi mu inganta rayuwarsu, mu karfafa musu gwiwa, don ganin rayuwar tasu ta inganta. Maimakon haka, sai aka yi ta faman kafa musu dokokin kama-karya. Wannan dalili ne yasa, aka wayi gari gwamnatin da aka kafa da niyyar cimma muradun bai-daya na sojoji, ta koma ta wasu ‘yan tsirarun mutane masu taurin kai”, in ji Babangida.
Ya bayyana cewa, “Yawancin juyin mulkin soja, muna yi ne sakamakon yawan korafe-korafen al’umma, musamman Talakawan da suka shiga matsanancin halin rayuwa, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da aka yi ta faman fuskanta na yau da kullum”.
“Haka zalika, batun komawa amfani da tsohuwar hanyar aiwatar da musayar kayayyaki a kasuwanci na kasa da kasa, na nufin cewa; kwata-kwata ba a kama hanyar kawo karshen matsalolin tattalin arzikin a tsakanin al’umma ba”, in ji IBB.
Har wa yau, sanin kowa ne cewa; dokokin kama-karya, sun tauye ‘yancin walwalar jama’a kai tsaye, sannan kuma ga hukunci mai tsauri, kamar yadda ya bayyana a littafin.
Kazalika, kayayyakin masarufi da sauran bukatun yau da kullum, sun yi matukar karanci, duk dai a wancan lokaci na mulki Buhari, in ji Babangida.
A bangare guda kuma, Janar Babangida a cikin littafin nasa, ya zargi marigayi tsohon shugaban kasa; Janar Sani Abacha da laifin yunkurin kifar da gwamnatinsa ta karfi da yaji da kuma zargin laifin soke zaben shugaban kasa na shekarar 1993.
Badamasi, ya amince da aikata babban kuskure a lokacin da yake shugabancin Najeriya, na gaza yi wa Sani Abacha ritaya daga aikin soja.
A lokacin, Abacha shi ne babban hasfan tsaro; wanda ya kwace mulki tsawon wata uku, bayan Babangida ya ajiye mukaminsa na shugabancin kasa.
Babangida ya kara da cewa, duk da shi da Abacha abokan juna ne, amma a fili yake cewa; Abacha mutum ne mai wuyar sha’ani, wanda ke biye wa munanan zantukan da ke faruwa a tsakanin rundunar sojin Nijeriya.
“Na yi mamakin yadda shi da wasu mutane suke da mummunar fahimta a kaina tare da nuna cewa, ni ne matsala,” in ji Babangida”.
A cikin littafin nasa ya ce, Abacha ne ya kitsa yadda za a cire shi daga shugaban kasa. Sai dai duk da haka, bai sallame shi daga aikin soja ba, saboda gudun zubar da jini a cikin rundunar sojin.
“A lokacin kan jami’an rundunar soji a rarrabe yake, don haka; duk wani yunkuri a lokacin, ka iya haifar da mummunar matsala,” in ji Babangida.
“Abin ya kai ga idan na yi wani kuskure daga bangarena, zai iya jawo zubar da jini, saboda za a samu yunkurin yin juyin mulki.”
Wannan tsokaci da IBB ya yi a littafin nasa, ya ja hankalin iyalan marigayi Sani Abacha, da ta kai har guda daga cikin ‘ya’yansa; Sadik Abacha ya mayar masa da martanin cewa, ‘yan Nijeriya ba za su taba mantawa da kokarin da mahaifinsu ya yi a bangaren ci gaban kasa ba, sannan kuma za su ci gaba da yaba masa kamar yadda suka saba.
“Mahaifina Abacha, kai ne a koda-yaushe suke yi maka hassada da bakin ciki. Saboda haka, tarihi zai ci gaba da tunawa da kai a matsayin shugaba nagari, ko su yabe ka; ko su yi suka, a matsayina na da, ina alfahari da kai, domin kuwa dukkaninsu suna fatan kai wa rabin matsayinka”, in ji Sadik.
Bugu da kari, makudan kudaden da aka tara a wajen kaddamar da littafin, ya yi matukar jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan Nijeriya, domin kuwa Naira na gugar Naira har biliyan 17.5 aka tara wa tsohon shugaban kasar; don gina dakin karatu.
Har ila yau, Alhaji Aliko Dangote, Abdussamad Rabi’u, Janar TY Danjuma, Arthur Eze da sauran makamantansu, su ne wadanda suka tara wadannan makudan kudade; a matsayin gudunmawa, domin gina wannan katafaren dakin karatu na Janar Babangida.
Wanda ya fi kowa tarin dukiya a dukkanin fadin Afirka, Aliko Dangote, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan biyu tare kuma da alkawarin ci gaba da bayar Naira biliyan biyu-biyu tsawon shekara uku, wanda idan aka hada jimillarsu zai kama Naira biliyan takwas.
Sai kuma Alhaji Abdussamad Rabi’u, wanda ya bayar da Naira biliyan biyar; duk da cewa, IBB ya bayyana cewa; tuni ya fara bayar da tasa gudunmawar wajen ginin wannan daki na karatu.
Akwai kuma, tsohon hafsan soji kuma ministan tsaro; TY Danjuma da ya yi alkawarin bayar da Naira biliyan uku. Sai wani shahararren Dan kasuwa mai suna Arthur Eze, shi ma ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 500.
Haka nan, akwai wasu da dama su ma da suka bayar da wannan gudunmawa da kuma wadanda suka yi alkawari; duk dai a wajen wannan kaddamar da katafaren littafi na Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp