Nijeriya na da arzikin da za ta riƙa ɗaukar nauyin tafiye-tafiyen Tinubu — Minista
Published: 28th, January 2025 GMT
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare.
A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Ana kuma ci gaba da jefa ayar tambaya ko shin tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi suna haifar da ɗa mai ido ta hanyar kalato wa ƙasar wata riba.
Sai dai a yayin da ya bayyana a Shirin Politics Today na Gidan Talabijin na Channels, Ministan ya kare matakin tafiye-tafiyen da shugaban ke yi a kai a kai.
Ya bayyana cewa, duk da ƙorafe-ƙorafen da ake yi, a halin yanzu ma akwai buƙatar shugaban ƙasar ya ƙara yawan tafiye-tafiyen saboda muhimmancin hakan wajen janyo wa ƙasar alfanu.
Ministan ya ce ta hanyar inganta alaƙar Nijeriya da sauran shugabannin ƙasashen duniya ne Shugaba Tinubu zai ɗora ƙasar kan turbar zuwa tudun tsira.
“Irin wannan ƙididdigar ƙwazo da ake yi wa gwamnatin a halin yanzu ba daidai ba ne domin kuwa har yanzu sabon shugaba ne a Nijeriya la’akari da cewa a shekarar 2023 ya shiga ofis.
“Saboda haka yana buƙatar ya mu’amalanci takwarorinsa shugabannin ƙasashen domin ƙulla dangantaka da su.
“Ko a bayan nan mun ga yadda aka ci ribar hakan [tafiye-tafiyen] da ta janyo wa ƙasar nan zuba jari na kimanin dala biliyan 2 daga ƙasar Brazil. Saboda haka abin da zan ce a yanzu akwai buƙatar a ƙara yawan tafiye-tafiyen.
Tuggar ya musanta zargin cewa Nijeriya ba ta da wadataccen arzikin da a riƙa ɗawainiyar waɗannan tafiye-tafiyen.
“In dai dangane da wannan mas’ala ce Nijeriya tana da arziki. Duka nawa ake kashewa wajen tafiye-tafiyen idan an kwatanta da ribar da ake samu a hakan?
“Sannan duka nawa ake kashewa idan an kwatanta da waɗansu ayyuka da shugaban ƙasar ya aiwatar a dalilin hakan?
Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, Tinubu ya ziyarci aƙalla ƙasashen duniya 19 a tafiye-tafiye 32 da ya yi zuwa ƙetare.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yusuf Tuggar shugaban ƙasar
এছাড়াও পড়ুন:
Babu wanda ya hana Shettima shiga Aso Rock ba— Fadar Shugaban Ƙasa
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da karaɗe kafofin sada zumunta cewa sojoji sun hana mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shiga Fadar Shugaban Ƙasa.
Labarin da ya tayar da ƙura cewa sojojin sun tare ƙofar shiga fadar shugaban ƙasa da cewa umarni ne daga sama ya koma gidansa da ke makwabtaka da fadar shugaban kasa, zuwa lokacin da Shugaba Tinubu ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai ƙasar Faransa.
Wata sanarwa da Stanley Nkwocha, hadimin shugaban ƙasa kan yada labarai, ya fitar, ta ce, babu kashin gaskiya a labarin.
Sanarwar ta kara da cewa hasali ma, masu yaɗa labarin karya sun ƙirƙirar shi ne da nufin haddasa saɓani tsakanin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin nasa.