An Kammala Gwaje-Gwajen Wasan Kwaikwayo Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG Na 2025
Published: 28th, January 2025 GMT
An gudanar da gwajin wasan kwaikwayo karo na biyar na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025 jiya Lahadi.
Ya zuwa yanzu, an kammala dukkanin ayyukan share fagen shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025. (Safiyah Ma)
.এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Rasha Ta Sanar Da Tsagaita Bude Wuta Da Ukraine Na Tsawon Kwanaki Bikin Ester
Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude wuta na kwanaki uku na Ista, inda ya yi kira ga sojojin kasarsa da su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Ukraine ta karya yarjejeniyar.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki uku na Ista, yana mai kira ga sojojin kasarsa da su “ci gaba da kasancewa cikin shiri don yiwuwar keta yarjejeniyar tsagaita wutan daga bangaren Ukraine, a sanarwar da fadar Kremlin na fitar.
Putin ya fada a ranar Asabar cewa: “Tsarin tsagaita bude wuta zai nuna a fili gwamnatin Ukraine tana da ikon warware matsalar cikin lumana.”
Putin ya kuma jaddada cewa: A ko da yaushe Rasha a shirye take don warware rikicinta da Ukraine ta hanyar lumana, kuma tana maraba da muradin Amurka, China da sauran kasashe na ganin an cimma daidaito kan batun na Ukraine.