An Watsa Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Karon Farko A Najeriya
Published: 28th, January 2025 GMT
A ranar 25 ga wata, agogon Najeriya, ofishin karamar jakadiya kasar Sin dake Legas, da tawagar Sinawa wadanda ke kasar, sun gudanar da jerin ayyuka don yin maraba da murnar bikin Bazara na shekarar maciji bisa kalandar gargajiyar Sinawa. An gudanar da bikin nune-nunen abinci, da nune-nunen kayayyaki, da liyafar maraba bi da bi, wanda ya samu halartar mutane sama da 2,000 da suka hada da Sinawa dake kasar da abokai ‘yan Najeriya.
Kafin an fara liyafar a maraice, an watsa bidiyon dandanon shagalin murnar bikin Bazara na shekarar maciji na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, Kyan hoton bidiyon mai kayatarwa kuma mai cike da ma’anar kimiyya da fasaha ya matukar burge bakin da ke wurin, ya kuma tada sha’awa mai karfi na yawancin baki ‘yan Najeriya, masu kallo sun kalli bidiyon a tsanake kuma sun yi kyakkyawar tafawa ma bidiyon. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Diblomasiyyar Kasashen Rasha Da Amurka Zasu Sake Haduwa A Birnin Istambul A Gobe
Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu.
Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko. Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau.
A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana ruwa guda a ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da Mosco.
A ranar 18 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne a karon farko tun bayan fara yakin Ukraine jami’an diblomasiyyar kasashen biyu suka hadu a birnin Riyad na kasar Saudiya.