Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar mai a fadin kasar.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar ɗan wasan Nijeriya a Uganda

Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda.

A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan ya faɗo daga benen wani katafaren kanti.

Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa

Cikin wani dogon saƙo da Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na X, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

“Muna baƙin ciki da samun labarin mutuwar Abubakar Lawal. Wannan lamari ne mai ban tsoro wanda akwai ayar tambayoyi da neman ƙarin haske.

“Saboda mun gano bayanai masu cin karo da juma game da rasuwarsa; Na farko an yi iƙirarin cewa hatsari ne, kuma rahoton na biyu ya ce ya faɗo daga baranda.

“Wadannan rahotannin masu cin karo da juna sun nuna wani abu ne da ke da shakku game da rasuwarsa kuma na tuntubi hukumomin Nijeriya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) su mai da hankalinsu kan wannan mummunan lamari da ya faru a Uganda.

“Ina kira ga gwamnatin Nijeriya da Hukumar NFF da su binciki lamarin, su haɗa kai da gwamnatin Uganda domin a yi wa Lawal adalci.

“Ran Lawal ya cancanci a yi cikakken bincike kuma a yi adalci idan an samu wani da laifi.

“Allah Ya jikansa tare da bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.”

Haka kuma, sa’o’i bayan faruwar lamarin mai ban takaici, Shugabar Hukumar ’Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewar akwai “ababen zargi” game da mutuwar Lawal.

“Wannan abin takaici ne kuma kamar akwai rashin gaskiya. Muna buƙatar a gudanar da cikakken bincike. Kada a yi rufa-rufa ko kaɗan.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ka Cire Sarkin Kano Bayero Daga Fadar Nasarawa – Gwamnatin Kano Ga Tinubu
  • Yanzu Yanzu – Kotu Ta Soke Zaɓen Ƙananan Hukumomn Ribas
  • Sojojin Nijeriya Za Su Fara Karɓar N3,000 Kudin Abinci A Rana
  • Trump Ya Kawo Karshen Shirin Bunkasa Samar Da Wutar Lantarki A Afirka
  • Sojojin Iran Sun Kammala Atisayen Zulfikar 1403 Da Faretin Sojojin Ruwa
  • Jam’iyyar APC Ta Sahalewa Shugaba Tinubu Damar Neman Shugabancin Nijeriya A 2027
  • El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci 
  • Shugabannin Afirka Ta Kudu, Malaysia Da Colombia Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Laifukan Isra’ila
  • Amurka : Kungiyar DAWN Ta Bukaci ICC Ta Binciki Biden Kan Laifin Hada Kai Da Isra’ila A Laifukan Gaza
  • Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar ɗan wasan Nijeriya a Uganda