A Banza Man Kare: Barazana Da Takunkumi Sun Daina Tasiri
Published: 28th, January 2025 GMT
Yanzu shekarar ta 2025 muke ciki, kuma matakin da duniya ke daukawa wajen gudanar da al’amura ya bambanta da shekaru goma da suka gabata. Amma abin takaici shi ne, wasu har yanzu sun nace ma tsoffin dabaru, suna ganin barazanar haraji da takunkumi na iya mamaye duniya, na san kun riga kun san inda na dosa.
Mu dauki Rasha a matayin misali, lokacin da ta fuskanci dimbin takunkumi daga kasashen yamma a 2014 da 2022, da yawa sun yi hasashen durkushewar tattalin arzikinta. Maimakon haka, Rasha ta samar wa kanta mafita ta hanyar tsarin hada-hadar kudi na cikin gida wato SPFS, wanda ba ya bukatar tsarin hada-hadar kudi na yammacin duniya, wannan yunkurin ya yi wa tattalin arzikin Rasha garkuwa tare da aza harsashi na zurfafa dangantakar hada-hadar kudi da kawayenta kamar Turkiya, Kazakhstan, har ma da al’ummomi a Gabas ta Tsakiya, tare da yin watsi da tsarin kasashen Yamma. Hakazalika, Amurka ta hana Turkiya damar amfani da fasaha da wasu kayayyakin aiki na Amurka, kama daga jiragen F-35 zuwa jiragen sama marasa matuka. Sakamakon haka shi ne, a halin yanzu Turkiya na kera wasu daga cikin wadannan kayayyakin aiki da albarkatunta har ma ta fara fitar da kayayyaki zuwa wasu kasashen Gabas ta Tsakiya da Afirka. Haka ma kasashen BRICS su ma sun yi ta sake fasalin ka’idojin cinikayyar duniya. Sun koma ga amfani da nasu kudade wajen gudanar da kasuwanci a tsakaninsu, suna rage dogaro da dalar Amurka. Hakazalika, Brazil da Sin na yin cinikayya da kudaden kasashensu, matakin da Indiya da kawayenta na yankin suke koyi da su. Yanzu dai kan mage ya waye, kuma kasashen duniya sun fahimci cewa hadin gwiwar samun moriyar juna tare da dunkulewar duniya waje guda su ne mafita ga kalubalen da duniya ke fuskanta, kuma wannan shi ne makasudin kafa BRICS. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
China Da Amurka Sun Yarda Da Rage Harajin Kayayyakinsu Domin Sasanta Rikicin Kasuwanci
Idan aka ga tana da tasiri, ana iya tsawaita ko kuma daidaita matakin.
Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa wannan ci gaba zai iya taimakawa wajen farfaɗo da cinikayya tsakanin manyan ƙasashen biyu, kuma zai taimaka wa ƙasashe masu tasowa da ke dogara da su wajen kasuwanci da kayan masarufi.
Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China ya fara ne tun daga 2018 lokacin da kowanne ɓangare ke ƙara haraji a kan kayayyakin juna, lamarin da ya haifar da hauhawar farashi da rikicin masana’antu a duniya.
Matakin rage harajin da suka ɗauka yanzu na iya zama sabon shafi na fahimtar juna da haɗin gwiwa a tsakanin manyan ƙasashen biyu na duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp