Firaministan Sin Ya Tattauna Da Baki Kwararru Dake Kasar
Published: 28th, January 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gudanar da taron tattaunawa da wakilan baki kwararru wadanda ke aiki a kasar da wadanda suka samu lambar yabo ta Abota ta Gwamnatin Sin.
Yayin taron wanda ya gudana jiya Lahadi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, Li Qiang ya kuma mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar Sinawa da fatan alheri ga bakin kwararru, ya kuma godewa goyon baya da kulawar da suka dade suna bayarwa ga kokarin Sin na zamanantar da kanta.
Kwararrun wadanda suka hada da ’yan kasashen Birtaniya da Poland da Mali da Romania da Jamus da Pakistan, sun gabatar da jawabai kan maudu’i daban daban, kamar na kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki da musayar al’adu da kuma musaya tsakanin jama’a da raya kwararru da ma cudanyar kasa da kasa.
Mataimakin firaminista Ding Xuexiang ma ya halarci taron. (Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamandan IRGC Ya Gargadi Amurka Dangane Da Hari Kan Kasar A Ranar Qudus Ta Duniya
Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma tsawon mita 180. Sannan
Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka.
Dakarun na IRGC dai sun gudanar atisai a ranar Qudus ta duniya a cikin tekun na farisa tare da jiragen ruwan yaki manya-manya da kanana wadanda suka kai kimani 3000.
Babban kwamandan ya kammala da cewa babu wani jirgin leken asirin Amurka da ya shigo sararin samaniyar kasar Iran kuma ba zamu taba barin haka ya faru ba. Yace zasu kare kasashen daga duk wanda yake son shigarta ba tare da amincewrasu ba.