NAJERIYA A YAU: Dabarun Noma Don Samun Kuɗaɗen Shiga
Published: 28th, January 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Akan ce ‘Noma tushen arziƙi’ kuma mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya ƙoshi babban arziƙi ne.
Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwanninsu don sama wa kansu abincin da za su ci.
Sai dai masana na ganin da waɗannan mutane za su inganta wannan noma da sun sama wa kansu kuɗaɗen shiga. NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan hanyoyin da ’yan Najeriya za su iya bi don sama wa kansu kuɗaɗen shiga bayan sun noma abin da za su ci.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris
A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin.
Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza sun kashe akalla Falasdinawa 80 a ranar Lahadi.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an kai mutane 53 da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitoci a Gaza a ranar Lahadin, wato ranar farko ta bikin Eid al-Fitr.
Ma’aikatar ta kara da cewa, “har yanzu da yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan gine-gine, saboda masu ceto ba su iya kai musu dauki.
A ranar 18 ga Maris, ne Isra’ila ta sake dawo da kai farmaki Gaza wanda ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da ta fara aiki a watan Janairu.
Ana kuma tuhumar Isra’ila da laifin kisan kiyashi a gaban kotun kasa da kasa saboda yakin da ta yi da yankin.