Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana.

“Ya yi kira da a yi la’akari da halin da ake ciki don tabbatar da ci gaba da samar da muhimman ayyukan ci gaba da na jin kai ga al’ummomin da ke da rauni a duniya,” in ji Stephane Dujarric ga manema labarai.

” Ya ce akwai al’umomin da suka dogara da wannan tallafin,” inda ya kara da cewa Amurka na “daya daga cikin manyan masu ba da agaji” a duniya.

Kwanaki kadan bayan rantsar da shi, shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka, inda ya umurci dukkan hukumomin gwamnatin tarayya da su sanya dokar ta baci na tsawon kwanaki 90 kan taimakon ci gaban kasashen waje da kuma duba shirye-shiryen da ake da su.

“Manufar Amurka ita ce ba za a sake ba da wani taimakon kasashen waje ba ta hanyar da ba ta dace da manufofin ketare na sabon shugaban Amurka ba,”.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce an dakatar da duk wani tallafin kudade na shirye-shiryen ba da agajin kasashen waje ban da na manyan kawayenta a Gabas ta Tsakiya, wato Isra’ila da Masar.

Amma umurnin na ranar Juma’a ya kebance tallafin abinci na gaggawa da kuma abubuwan da ke da alaka.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasashen waje

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump

Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump.

Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin da keta haddin kundin tsarin mulki da ‘yancin jama’a.

Wannan shi ne karo na biyu a wannan wata da dubban mutane suka yi tattaki a titunan Amurka domin nuna bacin ransu kan yadda Trump ke gudanar da mulkin kasar.

Korafe-korafen masu zanga-zangar sun hada da korar baki daga kasar da korar ma’aikata da gwamnati ke yi da kuma zargin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki.

Kazalika masu zanga-zangar na nuna fishi kan irin ikon da Trump ya bai wa Elon Musk, attajirin duniya mai kamfanin Tesla – wanda ya kori ma’aikatan gwamnati sama da dubu 200, ya kuma rushe hukumomin agaji na Amurka da dama a duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yakin Ciniki Kalubale Ne Kuma Dama Ce Ga Nahiyar Afirka
  • Shettima Ya Gayyaci Shugaban NAHCON Da Mambobin Hukumar Kan Shirye-shiryen Hajjin 2025
  • Trump : “Mun yi ganawa mai kyau da Iran”
  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • Tsakanin Kafa Shingaye Da Gina Gada: Yadda Matakan Amurka Da Sin Suka Bambanta Sosai
  • Iran Ta Yi Watsi Da Barazanar HKI
  • Har Yanzu Ruhin Taron Bandung Yana Tare Da Mu Wajen Kara Karya Lagon Babakere
  • Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump
  • Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Duniya Ya Kara Fito Da Kyawun Kasuwar Sin
  • KOFIN DUNIYA: Za A Kara Yawan Kasashen Da Suke Bugawa Zuwa 64 A Shekarar 2030