Abba Ya Naɗa Mace A Matsayin Akanta-Janar A Kano, Ya Yi Sabbin Sauye-sauye
Published: 28th, January 2025 GMT
Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta.
Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar.
An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Gudanarwa.
Aikin sa shi ne kula da gudanar da ayyukan ma’aikatu.
Injiniya Abubakar Sadiq kuma an naɗa a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a Ƙauyuka (RUWASA).
An ɗora masa alhakin inganta samar da ruwa da tsabtace muhalli a yankunan karkara.
Haka kuma, an kafa kwamiti na musamman domin farfaɗo da Hukumar Sufuri ta Jihar Kano (Kano Line).
Sa’idu Abdullahi Shu’aibu zai jagoranci kwamitin a matsayin Shugaba kuma Muƙaddashin Manajan Darakta, inda za su duba tare da tsara ayyukan Kano Line cikin watanni shida masu zuwa.
Gwamna Abba ya yi kira ga dukkanin sabbin jami’an da aka naɗa da su jajirce tare da nuna ƙwarewa, amana, da gaskiya wajen gudanar da ayyukansu.
Ya sake jaddada muhimmancin rawar da za su taka wajen ci gaban Jihar Kano.
কীওয়ার্ড: Gwamnatin
এছাড়াও পড়ুন:
Kada Ku Bari Siyasa Ta Raba Ku – Shettima Ga ’Yan Siyasar Kano
An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp