Qassem : Al’ummar Labanon Ba Za Su Manta Da Irin Goyon Bayan Da Iran Da Iraki Ta Yi Musu Ba
Published: 28th, January 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce al’ummar kasar Labanon ba za su manta da irin goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Iraki ta yi musu ba a lokacin da Isra’ila ke kai musu hare-hare.
Sheikh Naim Qassem ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa kai tsaye a yammacin jiya Litinin.
“Nasarar Gaza ta al’ummar Falasdinu ce, da al’ummomin yankin da suka tallafa musu da kuma duk masu neman ‘yanci a fadin duniya.” Inji shi.
Sheikh Qassem ya jaddada cewa tsayin daka wani zabi ne na siyasa, kasa da kuma jin kai don fuskantar mamayar Isra’ila da ‘yantar da yankunan da ta mamaye.
Ya bayyana cewa an cimma manufofin da ke tattare da farmakin Operation Al-Aqsa wanda kungiyoyin gwagwarmaya na Gaza suka kaddamar a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Sheikh Qassem ya bayyana hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan Lebanon da zirin Gaza a matsayin wani harin wuce gona da iri da Amurka da wasu gwamnatocin kasashen yammacin duniya ke goyon bayansu.
Ya ce, kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa tana da hadin kai ta kuma cike gibin shugabanci cikin kankanin lokaci bayan kisan babban sakatarenta Sayyed Hassan Nasrallah a wani kazamin harin da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut a karshen watan Satumba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta
Kamar yadda ba a lokaci guda a ke gina dabi’u ba, haka nan ba zai yiwu a rusa su a lokaci guda ba. mutum na gina dabi’a ne ta hanyar yin mu’amala da mutane. Gina dabi’un na farawa daga shekarun yarinta, saboda a sannan ne a ke koyon al’adu, tarbiyya da girmama manya. Har zuwa mutuwan mutum ya na mu’amala ne da mutane ya na gina sabbin dabi’u.
Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da nufin zagi, a wurin iyaye yara ke fara koyo. Shi ne ya sa za ka ga wani ya zama gwani a zagi, kwararren gaske. Ba a sama ya samo dabi’ar ba, abin da ya taso ya ga a na yi a gidansu kenan. Wasu kuwa gidansu mutanen kirki ne, don haka ba su iya samun daman kwaikwayon zagi a gida.
Daga gida, lokacin da yaro ya fara wayo, ma’ana zai yiwu a kyale shi ya rika fita waje, sannan ya kai shekarun fara zuwa makaranta. Wasu unguwarsu ‘G.R.A’ ne, babu hayaniya; ba irin unguwannin nan ba ne da a ke cakude da juna. A nan, dabi’un yaransu sun fi samuwa a mu’amalar da yaran ke kwaikwayo daga iyaye.
A irin unguwannin da a ke cakude, ma’ana wadanda yawanci ma gidajen haya ne masu mutane rututu, ya na wahala a iya saita dabi’un yaro. Na farko yaro zai rika kwaikwayon dabi’un iyayenshi, sannan zai rika kwaikwayon na ‘yan hayan gidansu, sannan zai rika kwaikwayon na sauran yaran kan layi; da ya ke irin wannan unguwannin kofofi a bude su ke, yaro ko da rarrafe ya ke yi, zai iya fita kan layi. Wasu yaran ma, dabi’un da su ke kwaikwayo wa a kan layi, ya fi karfin sanin iyayensu. A irin wadannan unguwannin mutane sun fi saurin diban dabi’u, masu kyau da marasa kyau.
Idan yaran wadanchan unguwannin ‘G.R.A’, suka fara zuwa makaranta, za su iya haduwa da yaran unguwannin da a ke cakude da juna. A makaranta za su fara musayar dabi’u a tsakanin juna. Mutum ya na kwance a gida, ya yi tsammanin dabi’unshi da na matarshi da mutanen cikin gida kadai dansu ke kwaikwaya, bai san cewa ya na kwaikwayo wasu daga mu’amalarshi da wasu yara a makaranta ba. wannan na faruwa hatta a makarantun Islamiyyoyi.
Ba kawai a yarinta a ke gina dabi’u ko kwaikwayonsu ba, kowanne mataki na rayuwa a na sake kwaikwayon dabi’u ne da gina sabbi. Wani zai taso har ya balaga da dabi’u masu ban sha’awa da burgewa, amma da zaran ya fara makarantar Sakandare ko gaba da Sakandare, sai yanayin mu’amalarsa ta chanza, saboda haduwa da zai yi da wasu sabbin mutane wadanda suka fito daga wurare mabambanta. Idan ba a yi sa’a ya hadu da abokan arziki ba, sai ya hadu da wadanda a hankali za su gina mishi dabi’un shaye-shaye, ko kuma neman mata.
Musamman a jami’o’i, wata yarinyar za ta zo daga gidansu da dabi’un kwarai, babu ruwanta da sa suturar banza. Yawancin irin wadannan ‘yan matan, a kan hada su zama dakin ‘Hostel’ daya da su. Tun kafin ta fara halartan azuzuwa don daukan darasi, tun kafin ta san sauran mutanen ajinsu, da wadannan abokan zaman nata za ta fara mu’amala. Idan ba a dace ba, a hankali za su koya mata dabi’ar fita babu lullubi ballantana hijabi. Idan samarinsu sun zo zance, sai su rika takura mata a kan ta yi musu rakiya, har watarana abokin saurayin ya ganta ya ce ya na so, shi kenan ita ma ta shiga shirgin.
Kowacce irin dabi’ar mutum, idan a na son a rusa ta, ba a garaje, ba a gaggawa, ba kuma a nuna kosawa. A hankali za a rika nunawa wannan dabi’ar rashin dacewarta, da kuma nakasunta. Ba a rusa dabi’a da karfi ko da fada, ba a rusa ta da iko ko nuna isa. Dabi’u sun fi bukatar lalama da sassauci.
Kafin ka iya rusa dabi’ar mutum, dole sai ka yi nazarin yadda ya ke kallon wannan dabi’a ta sa, ma’ana fahimtarsa dangane da dabi’ar. Idan Yaro ne wanda ke shaye – shaye, dole ne sai ka fahimci menene fahimtarsa dangane da shaye-shaye, tare da nazarin abubuwan da suka jefa shi zuwa ga shaye – shayen. Shin akwai wani abu da ya ke kauna? Idan akwai menene wannan abin? Shin ya na samun daman yin tunani, wanda ba a maye ba, a hankalinshi? Idan ya kan samu lokacin yin tunani ba tare da ya sha komi ba, sai ka fahimci wannan lokacin, a sannan ne za a iya fara aikin chanza mishi tunani.
Kafin mutum ya fara wannan dabi’a da a ke son rusawa, dole a baya ya na da wasu dabi’u, kuma ya na da wasu abokai wadanda a bayan ya ke mu’amala da su. Dole a na bukatar sannan wannan. Saboda idan dabi’ar ta yi kamari, dole ne sai an sake dawo mishi da rayuwar da ya yi a baya, an dawo mishi da tsofaffin abokai, sannan a shimfida musu tsarin yadda za su tafiyar da mu’amala a tsakaninsu, idan a ka bi matakan yadda suka dace a kan yi nasarar rusa dabi’ar da ba a so. Sai dai hanzari ba gudu ba, kwaikwayon dabi’a ya fi sauri a kan rusa ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp