Falasdinawa 300,000 Sun Koma Gaza Bayan Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Isra’ila
Published: 28th, January 2025 GMT
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas.
“Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan.
An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila.
An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki.
A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin na da bukatar tallafin gaggawa musamman tantuna da wurin kwanci da ruwa mai tsafta da abinci da kula ta kiwon lafiya da dai sauransu inji kungiyoyin agaji.
“Muna kira ga al’ummomin kasa da kasa, kungiyoyin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kasashen Larabawa dasu samar da wadanan kayayakin ga al’ummar falasdinu inji kungiyoyin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar RED CROSS Ta Duniya Ta Yi Allawadai Da HKI Saboda Kissan Likitoci 8 A Asbitin Rafah
Kungiyar bada agaji ta RED CROSS ta yi allawadai da HKI saboda kissan likitoci 8 a garin Rafah na kudancin gaza a ranar 23 ga watan Maris da muke ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya lahadi bayanda aka basu daman dauko gawakin likitocin wadanda suka rasa rayukansu a cikin watan Motar amblance ta daular marasa lafiya.
Labarin ya bayyana cewa lokitocin suna kan hanyarsu ta zuwa unguwar Hashasha inda HKI ta kai hare-hare kan Falasdinawa don basu taimakon gaggawa.
Banda haka sai da aka dauki mako guda cur da kashe likitocin kafin sojojin yahudawan su bada damar a dauki gawakin nasu.
Ya zuwa yanzu dai tun bayan fara yakin Tufanul Aksa falasdinawa dubu 50 da kari ne sojojin HKI suka kashe a gaza.