HausaTv:
2025-04-22@11:23:53 GMT

Ana Bikin Zagayowar Ranar Aiko Da Manzon Tsira (SAW)

Published: 28th, January 2025 GMT

Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as.

Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.

a.w) a lokacin yana dan shekara 40.

Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci.

Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci da kuma girmama jama’a, wadanda suka girme shi da ma wadanda ya girma.

Allah madaukain sarki ya aiko da sako zuwa ga bil adama, wanda ya zama sanadin shiririyar jama’a da dama a lokacinsa, mafi yawan wadanda suka muslunta tare da manzon Allah a Makka sun musulunta ne sakamakon kyawawan dabi’unsa, kamar yadda da dama daga cikin wadanda suka muslunta a Madiana bayan hijira sun karbi muslunci ne sakamakon kyawawan dabi’u da suka gani tare da manzon Allah, wadanda addinin ke koyar da dan Adam.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20

 

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), wacce da farko ta bayar da rahoton mutuwar mutum guda yayin aikin ceton a ranar Asabar amma a yau Lahadi, ta ce, adadin yanzu ya kai Biyar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Motar hatsi ta kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
  • Motar hatsi kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
  • Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 112
  • Bikin Easter : Paparoma Francis ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
  • Ango ya tsere tare da surukarsa
  • Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem
  • Fursunoni 9 Sun Tsere Daga Gidan Gyara Hali A Jihar Kwara, An Cafko Guda Daya
  • Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari?
  • Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20