Hadi Sirika ya ba wa kamfanin da bai cancanta ba kwangilar N2.8bn
Published: 28th, January 2025 GMT
Wani shaida ya bayyana wa kotu yadda tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Sanata Hadi Sirika ya ba wa kamfanin da bai cancanta ba aikin gyaran Filin jirgin Katsina a kan Naira biliyan 2.8.
tsohon Daraktan Sayayya ne a ma’aikatar, Musa Obinyan ya bayyana wa kotu cewa a lokacin da Hadi Sirika yake ministan ba wa Kamfanin Al Buraq Investment Ltd, aikin gyaran filin jirgin, alhalin kamfanin bai cancanci a ba shi aikin ba.
Musa Obinyan ya shaida wa Babbar Kotun Abuja cewa rufa-rufa aka yi aka ba wa Al-Buraq, sannan nemo kuɗin aikin aka yi daga wani wuri aka biya.
Ya ba da shaida ne a ci gaba da sauraron shari’ar da Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin (EFCC) take tuhumar Hadi Sirika da badaƙalar Naira biliyan 19.4.
Da kuɗin hayar gidana da ke Kaduna nake sayen abinci a yanzu — Buhari ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —BincikeHukumar EFCC na zargin Hadi Sirika da laifuka 10 da suke da alaƙa da almundahana a lokacin da yake ministan sufurin jiragen sama.
Daga cikin laifukan, ana zargin tsohon, da ba da kwangila ga kamfanin Enginos Nigeria Ltd mallakin ƙaninsa, Abubakar Sirika.
Obinyan ya ƙara da cewa an sanya Alburak da Enginos a matsayin abubuwa daban-daban a kasafin ma’aikatar, amma daga bisani aka gano cewa bayanansu ɗaya a sashen sayen kayayyaki na ma’aikatar.
A baya an gurfanar da Hadi Sirika tare da ’yarsa Fatima Hadi Sirika, da surukinsa, Jalal Sule Hamma tare da kamfanin Al Buraq Global Investment Ltd.
Kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Maris, 2025.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɓarayin waya a Kano
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago.
Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar SakkwatoSai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata.
SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin sayen wayoyin hannu da aka sata.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.
Rundunar ta gargaɗi ’yan kasuwa da su zama masu lura da abokan hulɗar da suke mu’amala da su, yana mai cewa akan samu miyagu da suke sojan gona a matsayin masu sayen kayayyaki a kasuwa.
Kazalika, rundunar ta yi kira ga duk wani ɗan kasuwa da irin haka ta faru da shi da ya gaggauta kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa.