Kotu ta hana ’yan sanda sake taɓa Muhuyi Rimingado
Published: 28th, January 2025 GMT
Babban Kotun Jihar Kano ta rundunar ’yan sanda sake kamawa, gayyata ko tsare Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Jihar Kano (PCACC), Magaji Rimingado.
Kotun ta ba a da umarnin ne bayan ƙarar da Babban Lauyan jihar Kano da hukumar PCACC da kuma Magaji Magaji Rimingado suka shigar.
Waɗanda ake ƙara su ne rundunar ’yan sandan Najeriya, Sufeto-Janar na ’yan sanda da Mataimakinsa Ma kula da Shiyya ta Ɗaya da Kwamishinan ’Yan Sanda Kano da ASP. Ahmed M. Bello da Bala Muhammad Inuwa.
Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu, 2025.
A ranar Juma’a ’yan sanda sun kama shugaba na hukumar da yamma, inda suka tsare shi na tsawon awanni, daga baya ba da belinsa da tsakar dare, tare da umartar sa ya kai kansa hedikwatar rundunar da ke Abuja ranar Litinin don amsa tambayoyi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu
A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci.
Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama.
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ya yi Allah wadai da kama Mahdieh Esfandiari, yana mai yin Allah wadai da “manufofin kasashen Turai” wanda “ya kunshi murde adawa da “kisan kare dangi” da Isra’ila ta yi a Gaza.
Ya kara da cewa ba a sanar da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris da kuma iyalan yarinyar ba.
A nasa bangaren, lauyan Mahdieh Esfandiari, Nabil Boudi, ya nuna rashin jin dadinsa kan kamun da aka yi wa wadda yake karewa.