Leadership News Hausa:
2025-04-23@06:15:11 GMT

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 4 Ƴan Gida Ɗaya A Abuja

Published: 28th, January 2025 GMT

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 4 Ƴan Gida Ɗaya A Abuja

Rundunar ƴansandan Abuja, ta bayyana cewa rashin samun labarin lamarin da wuri ne ya kawo jinkirin ɗaukar mataki.

Mun Fara Bincike – Ƴansanda

Kakakin rundunar ƴansandan Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni suka fara bincike domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ta ce: “Ƙarfe 1 na dare muka samu kiran gaggawa cewa ƴan bindiga sun kai hari Chikakore.

Nan take muka tura ƴansanda zuwa yankin. Bincike ya nuna cewa maharan guda bakwai ne, sun yaudari mai gidan har ya buɗe musu ƙofa.”

Ta kuma ce wata maƙwabciyarsu da ta yi ƙoƙarin taimaka musu ta ji rauni, kuma tana karɓar magani a asibiti.

Rundunar ta buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da bayar da haɗin kai wajen bincike.

Fargaba Kan Matsalar Tsaro a Abuja

Wannan harin ya jefa tsoro a zukatan mazauna yankin, musamman waɗanda suka sha fama da matsalolin tsaro a baya.

A farkon watan nan, wasu ƴan bindiga da ake sun tayar da abun fashewa a wata makarantar Islamiyya a ƙauyen Kuchibuyi, Bwari, inda mutane biyu suka rasa rayukansu.

Yankin Bwari, wanda ke maƙwabtaka da jihohin Kaduna da Neja, ya sha fama da hare-haren ƴan bindiga, ciki har da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Wannan ya sa mazauna yankin ke fargabar dawowar zaman ɗar-ɗar a rayuwarsu.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Hari Yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Sahel: CILSS ta yi gargadi game da sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin sahel

Kwamitin kasa da kasa kan yaki da fari a yankin Sahel (CILSS) ya yi wani gargadi na musamman kan sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin Sahel, wanda ke da hadarin yin illa nan gaba.

Shafin yanar gizo na CILSS ya bayar da rahoton cewa, “Kwananan kwararru kan yaki da fari sun fitar da sanarwar sake bullar farar kwarin dango a kasashen Sahel da dama.”

CILSS ta yi gargadin cewa “, wannan na iya haddasa matsala sosai a lokacin noma a yankin da ya riga ya kasance mai rauni’’.

Yayin da ake fuskantar wannan barazana, CILSS na ganin cewa, ya zama wajibi a ba da goyon baya mai dorewa ga kasashendake sahun gaba wajen fuskantar irin wannan matsala na yankin Sahel, wajen aiwatar da shirye-shiryensu na gaggawa, domin dakile duk wata matsalar fari da ka iya yin illa ga kakar noma mai zuwa a yankin Sahel.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sabuwar Ƙungiyar ‘Yan Bindiga Ta Addabi Jihohin Kwara Da Neja
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
  • Gwamna ya dakatar da basarake kan satar mutane da yankinsa
  • Sahel: CILSS ta yi gargadi game da sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin sahel
  • Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
  • Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja
  • An Yi Mummunar Arangama Da ‘Yan Bindiga A Sakkwoto
  • NDLEA Ta Kama Masu Sayar Da Kwaya Ga Ƴan Bindiga A Kano
  • Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue
  • Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas