Neja Ta fadada Shirin Inshorar Lafiya Ga Manoma Da Masu Rike Da Mukaman Siyasa.
Published: 28th, January 2025 GMT
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatin jihar na hada rijistar manoma da masu rike da mukaman siyasa a cikin shirinta na inshorar lafiya domin tabbatar da ayyukan kiwon lafiya ga daukacin ‘yan kasa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Minna, a lokacin da ya karbi bakuncin abokan hulda na ci gaba daga kungiyar Global Alliance for Vaccine Immunisation GAVI, UNICEF da WHO da suka je jihar domin bikin rufe taron GAVI da ke tallafawa tsarin karfafa tsarin PHC a jihar Neja.
Umar Bago ya ce manoma da masu rike da mukaman siyasa da makiyaya za a yi musu rajista ta ma’aikatar makiyaya sannan ya nuna cewa duk ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa za a yi musu rajista kari akan wasu su dubu dari biyu da hamsin da suka rigaya.
Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da yin rijistar haihuwar yara bisa manufofin shirin na UNICEF.
Sai dai ya bayyana cewa nan da watanni 6 ne za a kaddamar da shirin samar da allurar riga-kafi, domin ba da damar samar da magunguna na zamani zuwa yankunan masu nisa da lungunan jihar.
Shugaban Hukumar Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, Ibrahim Sesay ya bayyana shirin rajistar haihuwa a matsayin na asali ga kowane yaro wanda shine dalilin da ya sa aka samu rijistar haihuwa dari bisa dari a shekarar 2024 tare da yiwa yara sama da 400,000 ‘yan kasa da shekaru 5 rijista.
Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya Dr. Shyam Pathak ya yarda cewa shirin na shekaru 3 a jihar ya taimaka matuka wajen rage mace-mace da cututtuka ciki har da inganta samar da ayyukan kiwon lafiya ga marasa galihu.
Muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun hada da bayar da lambar yabo ta UNICEF ga Gwamna Mohammed Umar Bago saboda gudunmawar da ya bayar a fannin kiwon lafiya.
KARSHEN ALIYU LAWAL/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Inshora
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɓarayin waya a Kano
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago.
Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar SakkwatoSai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata.
SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin sayen wayoyin hannu da aka sata.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.
Rundunar ta gargaɗi ’yan kasuwa da su zama masu lura da abokan hulɗar da suke mu’amala da su, yana mai cewa akan samu miyagu da suke sojan gona a matsayin masu sayen kayayyaki a kasuwa.
Kazalika, rundunar ta yi kira ga duk wani ɗan kasuwa da irin haka ta faru da shi da ya gaggauta kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa.