Buk Ta Karbi Bakuncin Taron Tattaunawa Kan Aikin Jarida Na Bincike
Published: 28th, January 2025 GMT
Kwalejin Sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta hada kai da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya SNB domin gudanar da wani taron tattaunawa kan kalubalen aikin jarida na bincike da bayanai a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Taron wanda ya gudana a BUK, ya tattaro ‘yan jarida, malamai, da kwararru kan harkokin yada labarai, inda suka tattauna kan yanayin aikin jarida na bincike a yankin.
Taron dai na da nufin gano kalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin bunkasa aikin jarida na bincike a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
A jawabin sa na farko, shugaban SNB wanda kuma shine Shugaban jami’ar tarayya Kashere Gombe Farfesa Umaru Pate ya jaddada muhimmancin bayar da bayanai ta hanyar magance matsalar cin hanci da rashawa, shugabanci, da kalubalen ci gaba a yankin Arewa maso Yamma.
Tsohon mai watsa labarai Ado Warawa ya bayyana abubuwan da ya gani a aikin jarida na bincike, yayin da Farfesa Sulaiman Yar’adua na sashen sadarwa na BUK ya tattauna kan kalubalen da ke damun aikin jarida na bincike a yankin.
Yar’adua ya yi kira da a kara saka hannun jari wajen horar da ‘yan jarida da kuma tsauraran tsarin shari’a don kare masu aikin yada labarai.
Zauren ya ba da dama ga mahalarta don musanyar fahimta da shawarwari.
Sashen Sadarwa da Kungiyar Masu Watsa Labarai ta Najeriya sun yi alkawarin ci gaba da shirya irin wadannan tarukan don karfafa ayyukan yada labarai da kuma samar da rahotanni masu tasiri a Najeriya.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jarida Taro aikin jarida na bincike
এছাড়াও পড়ুন:
An Gayyaci Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Aragchi Taron Makamashin Nukliya A Amurka
Bayan taro na biyu tsakanin JMI da Amurka a birnin Roma na kasar Italiya a jiya Asabar an gayyaci ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi don gabatar da Jawabi a wani taro wanda mahukuntan kasar Amurka suka shirya.
Kamfanin dillancin labarai IP na kasar ya nakalto masu shirya taron na cewa an gayyace Abbas Arichi don gabatar da jawabin ne don muhuntan Amurka su ji ta bakin wadanda suka kore a sanin amfanin makamashin nukliya ta zaman lafiya da kuma tattaunawa a kansa.
Labarin ya nakalto wadanda suke gudanar da taron wato ” The Carnegie International Nuclear Policy Conference” wanda za’a fara a gobe litinin, na cewa taron yana taimakawa mahukuntan kasar Amurka sanin kan yadda jami’an diblomasiyya yakamata su fahinci abubuwan da suke da sarkakiya a cikin fasahar nukliya.
Har’ila yau ana son jin yadda Iran take gudanar da shirin ta makamacin Nukliya ta zaman lafiya a duk tsawon shekarun da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa mai yuwa ministan ya halarci taron ta hotunan bidiyo daga nan Tehran. Labarin ya kammala da cewa taron Amurka da Iran dangane da shirinta na makamashin Nukliya da aka kammala a birnin Ruma ne ya tada wannan bukatar ta jin bangaren Iran dangane da fannonin da ake sarrafa makamashin nukliya ta zaman lafiya.