An Fitar Da Jerin Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na Shekarar 2025
Published: 28th, January 2025 GMT
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya fitar da jerin shirye-shiryen shagalin murnar bikin bazara na bana a yau Talata. Shagalin na bana zai kunshi nau’o’in shirye-shirye daban-daban, kamar wake-wake da raye-raye da wasannin kokawa na gargajiya da na siddabaru da sauransu, domin murnar zuwan sabuwar shekarar gargajiya ta Sin tare da masu kallo dake fadin duniya.
A lokaci guda, wasu kafafen yada labarai 2,900 a kasashe da yankuna sama da 200 dake fadin duniya, za su kama tashoshin talabijin na CGTN na kasar Sin na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Rashanci da sauran dandamali dake amfani da harsunan waje har 82, wajen watsawa tare da bayar da rahotannin shagalin bikin bazara na bana.
Har ila yau, a karon farko, CMG zai hada hannu da kungiyoyin kafafen yada labarai na yankin Asiya da Pasifik da na yankin Larabawa da na Afrika da ma na Turai da Latin Amurka, wajen yayata shagalin bikin bazara na gidan talabijin na CCTV na kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
2024: Manyan Alkaluman Sufuri 2 Na Filayen Jiragen Sama Na Kasar Sin Sun Kafa Tarihi
A shekarar 2024, an kammala jigilar fasinjojin da yawansu ya kai biliyan 1.46 a filayen jiragen sama na kasar Sin yayin da yawan tashi da saukar jiragen sama ya wuce miliyan 12.4, adadin sun karu da kashi 15.9 bisa dari da kuma kashi 5.9 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Hakan ya nuna cewa, duka alkaluma masu alaka da harkokin sufuri sun kafa tarihi.
Kazalika, a ranar 21 ga wata, kungiyar filayen jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da kwalejin nazarin kimiyya da fasahar jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da sauransu sun fitar da “Rahoton kimanta ingancin hidimar filin jirgin sama na shekarar 2024”, inda rahoton ya ce, akwai daidaito da ci gaba a zirga-zirgar jiragen sama na yau da kullum a kasar Sin. A shekarar ta 2024, yawan zirga-zirgar jiragen sama na yau da kullum a kasar ya kasance kashi 87.1 cikin dari, wanda ya kai sama da kaso 80 cikin dari tsawon shekaru bakwai a jere. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp